logo

HAUSA

WHO ta yabawa ci gaban da Nijeriya ta samu wajen bibiyar masu cutar tarin fuka yayin da ake fama da COVID-19

2021-07-24 16:06:19 CRI

WHO ta yabawa ci gaban da Nijeriya ta samu wajen bibiyar masu cutar tarin fuka yayin da ake fama da COVID-19_fororder_src=http___www.tcrc.org.cn_UploadFiles_2017-03_0_201703271048227641&refer=http___www.tcrc.org

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yabawa kokarin tarayyar Nijeriya da matakan da ta dauka na bibiya da shawo kan cutar tarin fuka a kasar, yayin da ake fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a shekarar 2020.

Wata sanarwar da ofishin WHO a nahiyar Afrika ya fitar, ta ce alkaluma sun nuna cewa, an samu karuwar adadin masu cutar da ake samu a kowacce shekara, saboda kokarin da shirin yaki da cutar tarin fuka da kuturta na kasar (NTBLCP) da hadin gwiwar WHO da sauran wasu hukumomi suka yi.

A cewar sanarwar, a shekarar 2020 an ba da rahoton mutane 138,591 dake fama da cutar, adadin da ya karu da kaso 15, idan aka kwatanta da 106,533 da aka ba da rahoto a shekarar 2018 da 120,266 na 2019.

Sanarwar ta kuma ruwaito Chukwuemeka Anyike, shugaban shirin NTBLCP na Nijeriya na cewa, karuwar adadin na nufin an kara mayar da hankali wajen gano masu cutar da inganta daburu da matakan bibiya, yana mai cewa kasar na iya cimma burinta na bibiyar dukkan masu fama da cutar tare da kawo karshenta.

Ya kara da cewa, gano masu cutar na da muhimmanci wajen rage matsin da cutar ke haifarwa a kasar, saboda Nijeriya na da sama da mutane 440,000 dake kamuwa da cutar, inda kuma ake kasa gano sama da 300,000 a kowacce shekara. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha