logo

HAUSA

A karon farko za a yi amfani da fasahar Cloud wajen watsa gasar wasannin Olympics na Tokyo ga masu kallo

2021-07-23 13:55:48 CRI

A karon farko za a yi amfani da fasahar Cloud wajen watsa gasar wasannin Olympics na Tokyo ga masu kallo_fororder_0723-Tokyo-Faeza

Yayin da za a bude gasar wasannin Olympics ta Tokyo a yau da dare,  shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya Thomas Bach, ya ce a karon farko, za a yi amfani da fasahar Cloud wajen watsa wasannin.

Ya ce sabuwar fasahar da kamfanin Alibaba na kasar Sin ya samar, ya amfanawa wasannin da ma kwamitinsa ta fannoni da dama. Ya ce fasahar 3D da za a yi amfani da ita a dandalin watsa wasannin za ta samarwa ’yan kallo wata sabuwar hanyar more kallo. Ya kuma kara da cewa, wasannin na wannan karo wani muhimmin mataki ne na shiga babin amfani da fasahar zamani. (Fa’iza Msutapha)