logo

HAUSA

An gano kwayoyin yaki da cutar Covid-19 a samfuran jini da aka dauka kafin barkewar annobar a kasar Italiya

2021-07-22 16:55:31 CRI

An gano kwayoyin yaki da cutar Covid-19 a samfuran jini da aka dauka kafin barkewar annobar a kasar Italiya_fororder_fcfaaf51f3deb48fb11fe6d4fc59ed212df57810

Rahotanni daga jaridar Financial Times ta Burtaniya na cewa, masana kimiyya da ke cibiyar nazarin ciwon sankara ta birnin Milan(IstitutoNazionaleTumori) sun bayyana a wata mukalar da suka wallafa a ranar 19 ga wata cewa, wasu dakunan gwaji biyu sun sake gudanar da bincike a kan wasu samfuran jini da aka dauka kafin barkewar annobar Covid-19, inda aka gano kwayoyin yaki da cutar Covid-19, wadanda galibi a kan gano kwayoyin ne a jikin mutanen da suka harbu da cutar. Binciken na iya haifar da ce-ce-ku-ce dangane da ko cutar ta yadu a kasar ta Italiya ko sauran wasu sassa, kafin cutar ta bulla a birnin Wuhan na kasar Sin a watan Disamban shekarar 2019.(Lubabatu)