logo

HAUSA

Palastinawa sun bukaci kasashen Turai su kauracewa cinikayya da Isra’ila

2021-07-22 14:17:00 CRI

Palastinawa sun bukaci kasashen Turai su kauracewa cinikayya da Isra’ila_fororder_0722-Ahmad4-Palasdinu

Shugaban jam’iyyar Fatah ta al’ummar Palastinawa Mahmoud Abbas, ya sanar cewa, kasar Palastinu ta bukaci gwamnatocin kasashen Turai da su haramtawa kamfanoninsu yin huldar cinikayya da Isra’ila ta mamaye a yankunan dake karkashin ikon Palastinawa.

A cewar sanarwar, lokaci ya yi da ya kamata gwamnatocin kasashen Turai su aiwatar da dokokin kasa da kasa wajen katse dukkan wasu huldodin kasuwanci da yankunan Isra’ila ta mamaye a yankuna mallakin al’ummar Palastinawa.

A ranar Litinin, kamfanin Ben & Jerry, dake zaune a Amurka wanda ke samar da askirim, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, zai dena sana’ar sayar da askirim a yankunan da Isra’ila ta mamaye dake yammacin kogin Jordan da yankunan gabashin Kudus.

Isra’ila ta fara yin mamaya a yankunan yammacin kogin Jordan da gabashin Kudus ne a lokacin yakin yankin gabas ta tsakiya a shekarar 1967, kuma suna rike da ikon yankunan tun daga wancan lokacin. Mamayar da Yahudawa ke yiwa yankunan tamkar saba dokokin kasa da kasa ne wanda galibin kasashen duniya suka amince da su. (Ahmad)