logo

HAUSA

Masana na kasa da kasa sun mai da hankali kan kiyaye wuraren tarihi da ke cikin birane tare da tabbatar da dauwamammen ci gaba

2021-07-21 14:20:45 CRI

Masana na kasa da kasa sun mai da hankali kan kiyaye wuraren tarihi da ke cikin birane tare da tabbatar da dauwamammen ci gaba_fororder_16267657678759

Yanzu haka taro karo na 44 na kwamitin kula da wuraren tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO, na gudana a Fuzhou, babban birnin lardin Fujian na kasar Sin, kuma a gefen wannan taron, an gudanar da karamin taro game da “kiyaye wuraren tarihi da ke birane tare da samun dauwamammen ci gaba”, inda masana kimanin 120 na kasa da kasa suka tattauna batun bunkasuwar birane da ma kiyaye wuraren tarihi. Wakiliyarmu Lubabatu na dauke da karin haske.

Bana shekaru 10 ke nan da hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO ta kaddamar da takardar shawarwari dangane da kiyaye wuraren tarihi da ke cikin birane. Mahalarta taron sun bayyana cewa, dunkulewar tattalin arzikin duniya na haifar da illa ga al’adu da wuraren tarihi dake wasu tsoffin birane, abin da ya sa wasu birane suka rasa abin da ya bambanta su da wasu. Don haka, kiyaye tsoffin birane tare kuma da samun dauwamammen ci gaba, ya zama kalubale na bai daya da ke fuskantar kasa da kasa. Malam Wei Qing, babban sakataren kwamitin nazarin al’adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakani karkashin kungiyar kiyaye wuraren tarihi na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu wasu fasahohi a wannan fanni, yana mai cewa,“Ba kawai fasahohin kimiyya ake bukata wajen kiyaye wuraren tarihi ba, a’a, abin da ake bukata shi ne wani cikakken tsari na kula da su. A nan kasar Sin, an bullo da wani cikakken tsari da ya kunshi yadda gwamnati take kula da su.”

A yayin taron, masana na kasa da kasa sun ba da misalai da biranen Beijing da Roma da Kyoto da Brasilia ta fannin kare wuraren tarihi, don tattauna matakan da suka dace na kare wuraren tarihi a cikin birane. Madam Teresa Patricio, shugabar majalisar kula da wuraren tarihi na kasa da kasa, ta gabatar da jawabin cewa,“Ya kamata mu yi amfani da fasahohi na zamani, kana mu mai da hankali a kan al’umma, ta haka za mu iya amfana ta fannonin al’adu da zaman al’umma da muhalli da ma sauran fannoni daban daban. Hakan nan kuma wuraren tarihi da ke cikin biranenmu za su iya dorewa.”

Baya ga haka, Mr. Qin Lei, mataimakin shugaban lambun shakatawa na sarakunan gargajiya da ke birnin Beijing, wato Summer Palace a Turance, ya ce,“Wuraren tarihi su ne tushen tabbatar da dauwamammen ci gaban birane. Don haka, ya kamata a shigar da su tsarin gidajen al’umma ta hanyar shirya wasu harkoki da kuma yi kirkire-kirkiren al’adu da fasahohi, don a hada su da tsarin rayuwar al’umma, haka nan kuma za a iya kara kiyaye su da ma yayata su.”

An dai bude taron na wannan karo ne a Jumma’ar da ta gabata. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kuma aika wasikar taya murna ga taron. A cikin wasikar, Xi Jinping ya nuna cewa, al’adun duniya da kayayyakin tarihi da aka gada daga kaka da kakkani, babban ci gaban bunkasuwar wayin kan Bil Adama ne da sauyin muhallin hallitu, kuma sun ingiza mu’ammalar wayin kan al’ummu daban-daban.

Xi ya jaddada cewa, Sin na fatan kara hada kai da kasashe daban-daban da kuma UNESCO, don kara yin mu’ammala da hadin kai, da kuma ingiza tuntubar juna a fannin wayin kai da ciyar da musayar al’adu gaba, za kuma ta goyi bayan sha’anin kiyaye kayayyakin tarihi da aka gada daga kaka da kakkani, ta yadda daukacin Bil Adama zai iya kiyaye wadannan kayayyakin da raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.

Taron wanda a baya, aka shirya gudanarwa a bara, amma aka daga saboda annobar COVID-19, zai gudana har zuwa ranar 31 ga wata, inda za a tattauna kan ajandar bara da ta bana. Zai kuma yi nazarin wuraren da za su shiga jerin wuraren tarihi da aka gada a duniya, ciki har da birnin Quanzhou na lardin Fujian dake bakin teku, da kuma tsohuwar cibiyar cinikayya ta ruwa ta kasar Sin. Har ila yau, kwamitin zai yi nazarin yadda ake kiyaye wurare da tuni suke cikin jerin sunayen.

A yanzu, Sin na da wurare tarihi 55 da suka shiga jerin sunayen na UNESCO, wanda ya sa ta zama a kan gaba da Italiya, ta fuskar mallakar yawan irin wadannan wurare.(Lubabatu)