logo

HAUSA

Xi Jinping ya zanta da ’yan saman jannatin Kumbon Shenzhou-12

2021-06-23 11:10:27 CRI

Xi Jinping ya zanta da ’yan saman jannatin Kumbon Shenzhou-12_fororder_xi-hoto

Yau da safe ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara cibiyar kula da harkokin sararin samaniya dake birnin Beijing, inda ya yi hira da ’yan saman jannati Nie Haisheng, Liu Boming da Tang Hongbo ta waya.

Xi Jinping ya ce, gina tashar sararin samaniya wani muhimmin aiki ne cikin harkar sararin samaniya ta kasar Sin, wanda zai samar da gudummawa ga dukkanin bil Adama a fannin amfani da albarkatun sararin samaniya cikin lumana. Ya ce, “ku ’yan saman jannati guda uku, kun zama wakilai na dukkanin masu himma da kwazo kan aikin sararin samaniya na kasar Sin, da fatan za ku karfafa hadin gwiwar dake tsakaninku, ku kuma kammala ayyukanku lami lafiya”. (Maryam)