logo

HAUSA

James Zhan: Yawan jarin kai tsaye da za a zuba a ketare zai karu bayan ya kai kasa a bana

2021-06-23 13:16:19 CRI

Jiya Talata, shugaban sashen zuba jari da harkokin kamfanoni na kungiyar ciniki da bunkasuwa ta MDD (UNCTAD) James Zhan ya yi bayani kan rahoton “yanayin zuba jari a kasasen duniya na shekarar 2021” da kungiyar UNCTAD ta fitar a kwanan baya.

James Zhan: Yawan jarin kai tsaye da za a zuba a ketare zai karu bayan ya kai kasa a bana_fororder_James-hoto

Ya ce, a bana, yawan jarin da za a zuba a ketare kai tsaye zai karu bayan ya kai kasa, kuma karuwar adadin za kai 10% zuwa 15%, amma, ya kara da cewa, akwai wasu kalubaloli a gabanmu.

Ya ce, a shekarar 2020, yawan jarin da kasashe masu arziki suka zuba a kasashen ketare kai tsaye ya ragu sosai, inda adadin ya kai 58%, kana yawan jarin da kasashe maso tasowa suka zuba a kasashen ketare kai tsaye ya ragu da 8%, sai dai adadin bai ragu sosai ba, domin akwai kudaden ketare masu yawa da suka shiga kasashen Asiya. Kana, jarin waje da kasashe tattalin arzikinsu ke bunkasa suka samu kai tsaye, ya karu daga 50% a shekarar 2019 zuwa kashi 2 bisa 3 a shekarar 2020.

Rahoton ya kara da cewa, a shekarar 2020, jarin da aka zuba a kasar Sin kai tsaye ya karu cikin sauri, inda adadin ya kai 6%. Lamarin da ya nuna babbar nasarar da kasar Sin ta cimma a fannin yaki da annobar cutar COVID-19, da farfadowar tattalin arzikin kasar cikin sauri. Kuma, manyan fannonin da aka fi zuba jari kai tsaye a cikinsu, sun hada da na fasahohi da kasuwancin yanar gizo da harkokin nazari. Sannan a matsayinta na kasar da ta fi zuba jari a kasashen waje a shekarar 2020, adadin jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen ketare, ya kai dallar Amurka biliyan 133. (Maryam)