logo

HAUSA

Wasu kasashen duniya sun goyi bayan kasar Sin a taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD karo na 47

2021-06-23 11:19:04 CRI

Jiya Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana ra’ayin kasar Sin dangane da goyon bayan da wasu kasashen duniya suka nuna wa kasarsa, a taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD karo na 47.

Wasu kasashen duniya sun goyi bayan kasar Sin a taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD karo na 47_fororder_kakaki-hoto

A jawabinsa yayin taron a madadin kasashe guda 65, wakilin kasar Belarus ya jaddada cewa, ya kamata a girmama ’yanci da mulkin kai na kowace kasa bisa ka’idar kasa da kasa, bai kamata a tsoma baki a harkokin cikin gidan wata kasa ba. Harkokin dake shafar yankin Hong Kong, da jihar Xinjiang da kuma jihar Tibet na kasar Sin, harkokin cikin gidan kasar Sin ne, bai dace sauran kasashen duniya su tsoma baki a cikin wadannan harkokin ba. Ya kamata mu martaba “kundin da ka’idojin MDD, da mutunta ’yancin kasashe na zabar hanyoyinsu na neman bunkasuwa, kana, ba za mu yarda da wadanda suke tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ba, domin cimma mugun burinsu na siyasa.

Kungiyar hadin gwiwar kasashen yankin Gulf wato GCC da wasu kasashe guda 20, su ma za su yi jawabi domin nuna goyon bayansu ga kasar Sin kan wannan batu.

Dangane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, yadda kasashe sama da 90 suke nuna goyon bayansu ga kasar Sin, ya nuna cewa, kowa ya fahimci karyar da wasu kasahen yammacin duniya suka yada domin tsoma bakin a harkokin cikin gidan kasar Sin bisa hujjar hakkin dan Adam. Tabbas, ba wasu kasahen yammacin duniya za su cimma nasara ba. (Maryam)