logo

HAUSA

Za a rufe majalisar dokokin Uganda saboda sake bullar COVID-19

2021-06-23 10:17:38 CRI

Za a rufe majalisar dokokin Uganda saboda sake bullar COVID-19_fororder_病毒-2

A jiya ne kasar Uganda, ta sanar da rufe majalisar dokokin kasar na tsawon makonni biyu, bayan sake bullar annobar COVID-19 a karon biyu a kasar.

Da take karin haske cikin wata sanarwa, magatakardar majalisar Jane Kibirige, ta bayyana cewa, za a rufe majalisar ce daga ranar 28 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yuli, domin ba da damar fesa maganin kashe kwayoyin cuta a gine-ginen majalisar dake Kampala, babban birnin kasar.

Rufe majalisar na zuwa ne, bayan da a makon da ya gabata, hukumar dake kula da harkokin majalisar ta sanar da cewa, ‘yan majalisa da ma’aikata sama da 100 sun kamu da cutar.

Kibirige ta ce, sake bullar cutar a karo na biyu, wadda ta harbi kaso 17.1 cikin 100 na al’ummar kasar, ya shafi majalisar dokokin, kamar sauran sassan kasar.

Alkaluman hukuma na nuna cewa, daga watan Maris na shekarar da ta gabata zuwa jiya, cutar ta harbi mutane 73,401 a kasar, baya ga mutane 714 da cutar ta halaka.(Ibrahim)