logo

HAUSA

Wakiliyar yankin Xinjiang ta gabatarwa kwamitin kular da harkokin hakkin Bil Adama na MDD ci gaban da yankin ke samu

2021-06-23 14:48:23 CRI

Wakiliyar yankin Xinjiang ta gabatarwa kwamitin kular da harkokin hakkin Bil Adama na MDD ci gaban da yankin ke samu_fororder_20190808103317368124

Mataimakiyar shugaban kungiyar kula da harkokin kimiya ta yankin Xinjiang Gulnar Wuful, ta ba da jawabi a lokacin da take tattaunawa da babban kwamishina na kwamitin kula da harkokin hakkin Bil Adama na MDD a yayin taron kwamitin karo na 47, inda a madadin tawagar wakilan gwamnatin kasar Sin ta bayyana ci gaban da yankin ke samu a fannin tattalin arziki, da jin dadin al’umma, da kare hakkin Bil Adama a shekarun baya-bayan nan, inda ta jaddada cewa, ba wanda zai lahanta yanayin kwanciyar hankali da hadin kai da ake ciki a yankin ko kadan.

Gulnar Wuful ta ce, babu matsalar nuna ta’addanci ko guda ta faru a yankin a cikin shekaru fiye da hudu a jere da suka gabata. Ana kuma samun bunkasuwar tattalin arziki mai inganci, al’ummun yankin na kara hada kai. Ana kuma tafiyar da harkokin addinai kamar yadda ya kamata. (Amina Xu)