logo

HAUSA

Tunisia ta karbi alluran rigakafin CoronaVac COVID-19 na Sin

2021-06-23 10:00:06 CRI

Tunisia ta karbi alluran rigakafin CoronaVac COVID-19 na Sin_fororder_疫苗

Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Tunisia, ya sanar da cewa, wani rukuni na alluran rigakafin CoronaVac COVID-19 na kasar Sin, ya isa kasar Tunisia ranar Litinin da rana.

Sanarwar ta ce, kasar Sin tana fatan hada kai da Tunisia, don taimaka mata ganin bayan wannan annoba nan da nan, da taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar, da kuma kare lafiyar al’ummar Tunisia.

Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar kasar Tunisia ta fitar da maraicen ranar, ta ba da rahoton sabbin mutane 2,478 da suka kamu da cutar, abin da ya kai adadin wadanda suka harbu da cutar a kasar dake yammacin Afirka zuwa 385,428. A cewar ma’aikatar, yawan wadanda cutar ta halaka, ya karu daga mutum 80 zuwa 14,118, sai kuma mutane 336,652 da suka warke daga cutar.(Ibrahim)