logo

HAUSA

Jakadan Afrika ta kudu dake Sin: Ya kamata kafofin yada labarai na kasashen yamma su yi watsi da bambancin ra’ayi kan kasar Sin

2021-06-23 10:25:55 CRI

Jakadan Afrika ta kudu dake Sin: Ya kamata kafofin yada labarai na kasashen yamma su yi watsi da bambancin ra’ayi kan kasar Sin

Jakadan kasar Afrika ta kudu dake Sin Siyabonga Cwele ya shedawa manema labarai na CMG cewa, kamata ya yi kafofin yada labarai na kasashen yamma, su yi watsi da bambancin ra’ayi kan jam’iyyar JKS, su zo kasar Sin su yi cikakken bincike a Sin don gabatar da labarai dai dai game da jam’iyyar JKS.

Siyabonga Cwele ya ce, a matsayinsa na jakadan kasar Afrika ta kudu dake kasar Sin, yana aiki a nan kasar, ya ganewa idanunsa yadda jam’iyyar take kokarin bautawa jama’arta, da kuma jagorantar al’ummun kasar samun bunkasuwa mai wadata. Ya ce, JKS tana kara karfi, da cika alkawarinta na aiwatar da shirye-shirye na samun bunkasuwa, da yi mata kwaskwarima ta hanyar zurfafa tunanin tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin. A sa’i daya kuma, jam’iyyar tana kokarin hada kan mutane daban-daban don tabbatar da cewa, ba a bar kowa a baya ba.

Siyabonga Cwele ya nuna cewa, Sinawa su kan ce “gani yi kori ji”, kamata ya yi kafofin yada labarai na kasashen yamma, su yi cikakken bincike yadda ya kamata game da kasar Sin, don gabatar da labarai na gaskiya, maimakon ra’ayinsu ya rufe ido. Ya kuma jaddada cewa, akwai hanyoyi da dama na samun bunkasuwa mai wadata a duniya, a don haka, ya kamata a yarda da ko wace kasa ta zabi hanyar da ta dace da halin da take ciki. (Amina Xu)