logo

HAUSA

WHO da Afirka ta kudu za su kafa cibiyar samar da riga kafin COVID-19 mRNA

2021-06-22 10:17:18 CRI

WHO da Afirka ta kudu za su kafa cibiyar samar da riga kafin COVID-19 mRNA_fororder_0622-yaya-02-COVID-19 mRNA

Gwamnatin kasar Afirka ta kudu da hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun shirin kafa wata cibiyar musayar fasaha, da nufin hada alluran riga kafin COVID-19mRNA.

Da yake karin haske yayin wani taron manema labarai ta kafar bidiyo, shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, WHO ta gabatar da shawarar kafa cibiyar samar da riga kafin COVID-19, har ma ta karbi shawarwari 50, rabi daga cikinsu, sun fito ne daga kamfanoni dake da sha’awar raba kwarewarsu.

Ya ce, cibiyar za ta taimaka wajen sanya nahiyar Afirka a turbar dogaro da kai, ta hanyar ba ta damar samar da riga kafi nata na kanta.

A nata jawabin, babbar masaniyar kimiyya a hukumar WHO Soumya Swaminathan, ta bayyana cewa, cibiyar da ake fatan kafawa, za ta baiwa Afirka ta kudu damar kirkiro alluran riga kafi cikin watanni 9 zuwa 12 masu zuwa. (Ibrahim)