logo

HAUSA

CSCEC Ya Kammala Gina Babban Gini Mafi Tsayi A Afirka

2021-06-22 11:23:22 CRI

CSCEC Ya Kammala Gina Babban Gini Mafi Tsayi A Afirka_fororder_masar.JPG

CSCEC Ya Kammala Gina Babban Gini Mafi Tsayi A Afirka_fororder_Sin.JPG

CSCEC Ya Kammala Gina Babban Gini Mafi Tsayi A Afirka_fororder_sin02.JPG

Kwanan baya, kamfanin CSCEC na kasar Sin ya kammala aikin gina babbar cibiyar kasuwanci dake sabuwar hedkwatar tafiyar da harkokin gwamnatin Masar a hukumance. Mazauna wurin suna kiran wannan babban ginin da ake ci gaba da yi masa ado “babban gini mafi tsayi a nahiyar Afirka”.

Aikin gina cibiyar kasuwanci da ke sabuwar hedkwatar tafiyar da harkokin gwamnatin kasar Masar, wanda ke da nisan kilomita 50 daga gabashin birnin Alkahira, hedkwatar Masar, yana daya daga cikin muhimman ayyukan da aka tanada cikin shawarar “ziri daya da hanya daya”. Ana fatan kammala aikin a shekarar 2023. Reshen kamfanin CSCEC a Masar ne ya gudanar da aikin ginin babban ginin da ke alamta cibiyar. Fadin babban ginin ya kai murabba’in mita dubu 65, ciki hadda benaye 78 a sama da doron kasa da kuma benaye 2 a karkashin kasa wadanda fadinsu ya kai murabba’in mita fiye da dubu 260.

Yayin bikin murnar kammala gina babban ginin da aka gudanar a ranar 17 ga wata, ministan kula da harkokin gidaje na kasar Masar Asim Al-Jazzar, da shugaban reshen kamfanin CSCEC a Masar Chang Weicai da wasu manyan mutane na kasashen Sin da Masar sun kammala aikin zuba simintu na karshe kan babban ginin tare.

A yayin bikin, Wei Jianxun, babban manajan gudanarwa mai kula da aikin ginin babban ginin da ke alamta cibiyar kasuwancin ya yi karin bayani kan yadda ake gina wannan babban gini, inda ya ce, “Yanzu muna bene na 52 na babban ginin, wanda tsayin da ke tsakanin benen da doron kasa ya kai mita 251.4. Dazun nan mun zuba siminti na karshe cikin babban bututun mai tsayin mita 373.2 da ke cikin wannan babban gini mafi tsayi a nahiyar Afirka. Kana tsayin da ke tsakanin kololuwar babban ginin da doron kasa ya kai mita 385.8 baki daya. Kammala gina babban bututun ginin, ya samar wa Masar wata kyakkyawar damar shiga sabon karni, haka kuma ya kasance wani abin tarihin da ke shaida kokarin da kasashen Sin da Masar suka yi cikin hadin gwiwa, har ila yau ya ba da nasa gudummowa wajen aiwatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’.”

A jawabinsa yayin bikin, ministan kula da harkokin gidaje na kasar Masar Asim Al-Jazzar ya nuna godiya da yabo kan kokarin da bangaren Sin yake bayarwa kan wannan aiki, ya nuna cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Masar da Sin a sassa daban daban za ta zama babban karfin raya tattalin arziki, inda ya ce, “Yau mun gane wa idanunmu sakamakon da Masar da Sin suka samu ta hanyar yin hadin gwiwa da kokari tare. Mun yi imani da cewa, babban ginin da aka kammala ginawa a yau, zai zama sabuwar alamar Masar. Kila masu aikin gine-gine na Masar da Sin za su yi bayani kan wannan aiki ta fuskar gine-gine. Ni kuma zan gaya muku cewa, yau mun gane wa idanunmu wannan sakamakon hadin gwiwar kasashen 2. Nan gaba akwai ayyuka da dama da kasashen 2 suke bukatar ci gaba da gudanarwa bisa hadin gwiwarsu.”

Chang Weicai, babban manajan reshen kamfanin CSCEC a Masar ya yi nuni da cewa, kamfanin na CSCEC ya shafe shekaru 38 yana yin kasuwanci a Masar. Bangarorin Sin da Masar sun hada kai a muhimman ayyuka masu dimbin yawa a Masar, ciki hadda babban ginin, wadanda suka kara azama kan kara samar da guraben aikin yi da raya masana’antun wurin a Masar, inda ya ce, “Yayin da ake tinkarar barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, kamfaninmu yana hada kai da gwamnatin Masar a fannonin tabbatar da zaman rayuwar al’umma, samar da guraben aikin yi, da kara azama kan ayyukan samar da kayayyaki. Mu da abokan huldarmu a Masar muna taimaka wa juna kafada da kafada, a kokarin tabbatar da hadin gwiwar Sin da Masar ta fuskar karfin samar da kaya, da farfado da tattalin arzikin Masar. A shekarar 2021, ake cika shekaru 65 da kafa huldar jakadanci a tsakanin Sin da Masar. Za mu mayar da wannan babban gini a matsayin wani sabon mafari, za mu ci gaba da hada kai da sassa daban daban cikin sahihanci, za mu samu ci gaba tare, a kokarin tabbatar da gudanar da aikin gina cibiyar kasuwancin yadda ya kamata, za a kammala aikin a daidai lokacin da aka tsara. Za mu ba da gudummowarmu wajen tabbatar da manufar kasar Masar ta shekarar 2030, da raya cibiyar kasuwancin da babu irinta a yankunan Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka.” (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan