logo

HAUSA

Sabon shugaban Iran: Wajibi ne Amurka ta janye takunkumin da ta kakabawa kasar

2021-06-22 10:41:45 CRI

Sabon shugaban Iran: Wajibi ne Amurka ta janye takunkumin da ta kakabawa kasar_fororder_0622-yaya-04-Raisi

Sabon shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, ya bayyana a jiya Lininin cewa, tilas ne kasar Amurka ta janye dukkan takunkumai na babu gaira babu dalili da ta kakabawa kasarsa, ita kuma Turai ta martaba shadurran da suka cimma karkashin yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015.

Yayin jawabinsa ga abokan huldar Iran na Turai, wadanda ke cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar, shugaba Ebrahim Raisi ya bayyana cewa, ya kamata su yi watsi da matsin lamba da manufofin ketare na Amurka, yana mai jaddada wajibcin cika alkawarun da suka yi karkashin yarjejeniyar.

Yana mai cewa, Iran za ta sasanta ko dai manufofinta na shiyya ko na tsaron kasa da bangarori na ketare.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa, ko a shirye yake zai gana da shugaban Amurka Joe Biden, idan har Amurkar ta janyewa kasarsa dukkan takunkuman da ta kakaba mata, da ma cika bukatun da Iran din ta gabatar mata, sai Raisi ya ce “a’a”.

A ranar Asabar da ta gabata ne, ma’aikatar cikin gida ta kasar Iran, ta sanar da cewa, Raisi, wanda ke zama babban jami’in shari’ar kasar, ya lashe zaben shugabancin kasar Iran ne, da sama da kaso 60 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada. (Ibrahim Yaya)