logo

HAUSA

Amurka ba ta da hurumin sukar kasar Sin game da zakulo asalin cutar COVID-19

2021-06-22 21:50:26 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce ko kadan, Amurka ba ta da hurumin sukar kasar Sin game da zakulo asalin cutar COVID-19, ko yiwa Sin matsin lamba. Kaza lika Amurka ba za ta iya wakiltar sauran sassan duniya ba, wajen bata sunan kasar Sin, game da binciken asalin cutar COVID-19.

Zhao Lijian wanda ya bayyana hakan, lokacin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa, a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau Talata, inda ya ce Sin na bukatar a gudanar da cikakken bincike, don gano asalin cutar COVID-19 a Amurka, da dalilai, da kuma sassan da ya kamata a kama da laifin kin daukar matakan da suka dace, yayin da cutar ke bazuwa a Amurka.

Kaza lika a banciki matsalolin da suka auku a cibiyar gwaje gwaje ta Fort Detrick dake Amurka, da ma sauran wasu cibiyoyin gwaje gwaje sama da 200 mallakin kasar ta Amurka dake kasashen ketare.

Kalaman Zhao dai, tamkar martani ne ga tsokacin da sakataren watsa labarai na fadar White House Jen Psaki yayi, masu kunshe da sukar kasar Sin.  (Saminu)