logo

HAUSA

Ministan Yada Labarai Da Al’Adun Najeriya Ya Tayawa Sin Murnar Cika Shekaru 100 Da Kafuwar JKS

2021-06-22 10:59:07 CRI

Ministan Yada Labarai Da Al’Adun Najeriya Ya Tayawa Sin Murnar Cika Shekaru 100 Da Kafuwar JKS_fororder_微信图片_20210622091755

Ministan yada labarai da al’adun kasar Najeriya Lai Mohammed ya wallafa wani bayani a jaridar “The Dawn”, inda ya taya kasar Sin murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Yayin da ya ambaci ci gaban da jam’iyya ke samu, minista ya nuna jinjina matuka. Ya ce, wata jam’iyya ta samu ci gaba mai dorewa a cikin shekaru 100, wannan abin alfahari ne. A cewarsa, a madadin gwamnatin Najeriya, yana taya JKS murnar cika shekaru 100 da kafuwa. Ya ce, ya taba shiga aikin kafa jam’iyya, kuma ya ga yadda jam’iyyu suka hade,  da yadda suka rushe, saboda haka ya san yana matukar wahala da jam’iyya ta samu ci gaba a cikin shekaru 100, ko wata jam’iyya dake iya yin haka, wannan abin fari ciki ne matuka.

A wannan muhimmin lokaci, minista ya jaddada cewa, muna da imanin cewa, jam’iyya JKS za ta kara samun babban ci gaba a nan gaba, a hannu  guda kuma, Najeriya za ta ci gaba da hada kai da gwamnatin kasar Sin da jama’arta.

Lai Mohammed kwararrai ne na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, kana tsohon kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasar, kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar, hakan ya sa shi zama mutum mai karfin fada a ji a fannin siyasa a Najeriya. (Amina Xu)