logo

HAUSA

An rantsar da sabuwar mataimakiyar shugaban kasa da firaministan Uganda

2021-06-22 11:17:00 CRI

An rantsar da sabuwar mataimakiyar shugaban kasa da firaministan Uganda_fororder_0622-yaya-05-Uganda

Jiya ne, shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ya rantsar da Jessica Alupo a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, da Robinah Nabbanja a mukamin firaminista kana shugaban gwamnati a majalisar dokokin kasar. Haka kuma a jiyan ne, shugaba Museveni ya rantsar da majalisar zartaswa da kananan ministoci, yayin wani biki da ya gudana a filin samun ’yancin kai na Kololo dake Kampala, babban birnin kasar.

Alupo, tsohon ministan Ilimin kasar, ya maye gurbin Edward Ssekandi da aka kora, sai kuma Nabbanja, tsohon karamin ministan lafiya mai kula da manyan ayyuka, wanda ya maye gurbin Ruhakana Rugunda.

Shugana Museveni ya ce, ya kamata sabuwar majalisar ministocin, ta daga matsayin Uganda zuwa matsayin kasa mai matsakaicin kudin shiga. Ya ce, duk da matsalar COVID-19 da kasar take fuskanta, za mu yi kokarin magance wannan matsala yadda ya kamata. A don haka, wajibi ne wannan gwamnati ta hidimtawa jama’a. (Ibrahim Yaya)