Yanzu Sinawa na fama da aikin girbin alkama
2021-06-22 10:48:07 CRI
A ran 19 ga watan Yuni, an fara aikin girbin alkama a wani kauyen dake lardin Shandong. Ga yadda manoma lardin Shandong suke amfani da na’ura wajen girbin alkama.
Alkaluman da hukumar kula da aikin gona da yankunan karkara ta lardin Shandong ta fitar sun nuna cewa, da misalin karfe 5 na yammacin ranar 19 ga wata, an yi nasarar girbe alkama masu tarin yawa daga gonakin da yawansu ya kai hektoci miliyan 3.48 a lardin Shandong, wato lardin dake zama matsayi na biyu wajen samar da alkama mafi yawa a nan kasar Sin. (Sanusi Chen)