logo

HAUSA

Kasar Sin ta kaddamar da jerin sunayen alluran riga-kafin COVID-19 da ta samar don fitarwa

2021-06-22 20:50:46 cri

A yau Talata ne kasar Sin ta fitar da jerin sunayen alluran riga-kafin COVID-19 da ta sarrafa don fitarwa waje, ciki har da hudu da tuni sun riga sun samu iznin sayarwa a cikin kasar, kuma biyu daga cikinsu sun samu yardar amfani da su a matakin gaggawa daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

A yau din, shugaban Sashin Kasuwancin Kasashen Waje na Ma’aikatar Kasuwanci ta kasar Sin Li Xingqian, ya yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin ta fitar da jerin sunayen allurar riga-kafin don fitarwa, ba wai kawai don kasancewar alluran riga-kafin kirar kasar Sin masu amfani ga duniya baki daya ba kadai, har da ma kasancewar hakan wani mataki mai matukar karfi, na inganta hadin gwiwar kasa da kasa don yaki da annobar.

Baya ga haka, Li Xingqian ya kuma nuna cewa, Ma'aikatar Kasuwancin Kasar Sin, za ta ci gaba da ba da tallafi da goyon baya ga kasashe daban daban, ta yadda za su iya sayen alluran riga-kafi kirar kasar, tare da daukar matakai na zahiri, don taimakawa alluran rigakafin, su zama masu amfani ga al’ummar duniya baki daya. (Bilkisu)