logo

HAUSA

Wakilin Sin ya kalubalanci kasashen duniya da su taimakawa Sudan ta kudu

2021-06-22 14:10:58 CRI

Wakilin Sin ya kalubalanci kasashen duniya da su taimakawa Sudan ta kudu_fororder_src=http___inews.gtimg.com_newsapp_match_0_11364578255_0&refer=http___inews.gtimg

Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Dai Bing ya kalubalanci kasashen duniya, da su taimakawa Sudan ta kudu. Dai Bing, ya yi wannan kiran ne, a jawabin da ya gabatar yayin taron kwamitin sulhun MDD kan batun Sudan ta kudu jiya Litinin.

Ya ce, Sin tana kira ga kasashen duniya da su yi la’akari da halin da Sudan ta kudu take ciki, da mutumta ikon mulkin kasar na gudanar da harkokinta, su kuma goyi bayan AU da kungiyar gwamnatocin gabashin Afrika da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya da su taka rawa mai yakini don baiwa kasar taimako yadda ya kamata.

Ya kara da cewa, kamata ya yi kwamitin sulhu ya amsa kiran da AU ta yi na ganin an kawar da takunkumin da aka kakabawa Sudan ta kudu, tare da bayyana aniyyarsa ta taimakawa kasar.

Ban da wannan kuma, ya kamata kasashen duniya su kara karfin baiwa Sudan ta kudu tallafin jin kai, don taimakawa kasar dakile cutar COVID-19, da samar mata allurar rigakafi, ta yadda za a kubutar da kasar daga mawuyancin hali da take ciki. (Amina Xu)