logo

HAUSA

Wakilin MDD: An samu ci gaba a Sudan ta kudu duk da damuwar tsaro

2021-06-22 10:33:36 CRI

Wakilin MDD: An samu ci gaba a Sudan ta kudu duk da damuwar tsaro_fororder_0622-yaya-03-Sudan ta kudu

Babban wakilin MDD a Sudan ta Kudu Nicholas Hayson, ya bayyana damuwa game da yanayin tsaro da ake fama da shi a kasar, duk da ci gaban da ya ce an samu.

A watan Mayun wannan shekara ce dai, gwamnati ta kafa wani kwamiti da aka dora masa alhakin sanya-ido da tsara shari’a na wucin gadi da sauran gyare-gyare a fannin shari’a. Shugaban kasar Salva Kiir, ya sake fasalta majalisar dokokin kasar tare da nada sabbin mambobi 550. Daga bisani a watan Mayu, shugaba Kiir da firaministan Sudan Abdalla Hamdok, suka kaddamar da shirin tsara kundin tsarin mulkin kasar na din-din-din a hukumance a birnin Juba, fadar mulkin kasar.

A ranar 9 ga watan Yuli ne, Jamhuriyar Sudan ta kudu, za ta cika shekaru goma da samun ’yancin kai. Yana mai cewa, abu mai muhimmanci shi ne, yadda kasashen duniya suka goyi bayan kasar cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da jaririyar kasar ke kokarin ganin ta samar da zaman lafiya da tsaro ga al’ummominta.

Sai dai a cewar Hayson, duk da ci gaban da aka samu a kasar, har yanzu a dunkule, yadda ake aiwatar da yarjejeniyar farfado da kasar, yana tafiyar hawainiya. Tsarin kafa majalisar dokokin kasar bai ga kammala ba. A hannu guda kuma, yadda za a kai ga kafa majalisar ministoci, da zabar kakakin majalisa duk sun tsaya cik. (Ibrahim Yaya)