logo

HAUSA

Japan Ba Ta Da Fasahar Tace Ruwan Dagwalon Nukiliya

2021-06-22 15:39:44 CRI

Japan Ba Ta Da Fasahar Tace Ruwan Dagwalon Nukiliya_fororder_微信图片_20210622153732

BY CRI Hausa

Gwamnatin Japan tana kokarin yada labarai cewa, matakin da ta dauka na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, ba zai kawo illa ga duniya ba. Amma, wani labarin da kafar yada labarai ta kasar Japan ta fitar, ya karya wannan batu.

Kafar yada labarai ta NHK ta ba da labari cewa, kamfanin TEPCO mai kula da aikin sarrafa ruwan dagwalon nukiliya, yana jin ra’ayin al’umma don neman fasaha da ta dace don tace ruwan, saboda ruwan na kunshe da sinadarin “tritium” mai gurbata muhalli. Ganin wannan labari, ya sa wasu suna zargin cewa, gwamnatin Japan ba ta da fasahar tace ruwan, kuma bai dace ta zubar da ruwan a cikin teku ba.

Tun a watan Afrilu ne, gwamnatin Japan ta yanke wannan shawara, abin da ya sa kasashe makwabta da ma al’ummun duniya, nuna matukar rashin jin dadi. Amma, Japan ba ta saurari shawarwarin kowa ba, inda ta yanke shawara yadda take so, ta rika yin karairayi don kawar da hankalin duniya, Wasu ‘yan siyasar kasar sun ce, ana iya shan wannan ruwa, amma ba ta misali yadda za a shan ruwan ba tukuna.

A tarihin, Japan ta taba kai hari kan wasu kasashe don mulkin mallaka, matakin da ya jawowa kasashe da dama barazanar jin kai, amma har zuwa yanzu ‘yan siyasar kasar ba su nemi gafara ba. Yanzu kuma, ta aiwatar da wannan mumunan shiri da zai kawo babbar illa ga al’ummar duniya. Kasashen duniya ba za su yarda da haka ba. (Amina Xu)