logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kwamitin kare hakkin Bil Adama da ya ingiza rarraba allurar rigakafin cutar COVID-19 cikin daidaito

2021-06-22 14:02:46 CRI

Zaunannen wakilin Sin a ofishin MDD dake Geneva na kasar Switzerland da sauran kungiyoyin kasa da kasa, Chen Xu a madadin kasashe 63 na duniya, ya yi kira da a rarraba allurar rigakafin cutar COVID-19 cikin daidaito. Chen Xu ya yi wannan kiran ne, a yayin taron majalisar kare hakkin Bil Adama ta MDD karo na 47 kan batun tinkarar cutar COVID-19, da shawarwarin masana kan kare hakkin Bil Adama,

Chen ya ce, allurar ita ce mataki mafi karfi wajen dakile cutar, a don haka, kamata ya yi ta zama abin da kowa zai samu a duniya. Sin da wadannan kasashe 63 na goyon bayan kirar da MDD ke yi ta rarraba allurar cikin daidaito, da kalubalantar dukkanin kasashe da su hada kai, tare da cika alkawarinsu, ta yadda za a taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun allurar da magance cutar cikin sauri. Ban da wannan kuma, an yi kira ga kasashe masu wadata da su hada kai da sauran kasashe, don taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun bunkasuwa mai dorewa da kawar da illar da cutar ke jawowa. (Amina Xu)