logo

HAUSA

Xi ya amsa wasikar da wasu daliban ketare dake karatu a jami’ar Peking suka rubuta masa

2021-06-22 13:48:35 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karfafawa daliban ketare dake karatu a jami’ar Peking gwiwa, da su kara fahimtar kasar Sin kamar yadda take a zahiri, sannan su kara sanar da jama’a irin tunani da kwarewar da suka koya, su kuma taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa abokantaka tsakanin al’ummomin kasashensu.

Xi, wanda har ila shi ne, babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya bayyana haka ne jiya Litinin, cikin amsar wasikar da ya rubutawa wakilan daliban ketare 45 da suka fito daga kasashe 32, wadanda ke karatu a jami’ar Peking. (Ibrahim)