logo

HAUSA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Sin: Za a ci gaba da kiyaye halastattun hakkokin kamfanonin kasar

2021-06-22 20:08:39 cri

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya jinjinawa matakin Ma'aikatar Kasuwancin kasar Amurka, na soke haramci kan kamfanin WeChat da na TikTok, ya kuma bayyana cewa, wannan mataki ne mai kyau a hanyar da ta dace. Ya ce gwamnatin kasar Sin ma za ta ci gaba da kiyaye halastattun hakkoki na kamfanonin kasarta.

Wasu rahotanni sun ce Ma’aikatar Kasuwancin Amurka ta bayyana a jiya Litinin cewa, za ta soke dokar da gwamnatin da ta shude ta kafa, game da haramta yin kasuwanci, kan kafofin sada zumunta na kasar Sin, ciki har da WeChat da TikTok. (Bilkisu)