logo

HAUSA

An kusa cimma matsaya a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran

2021-06-21 11:29:49 CRI

An kusa cimma matsaya a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran_fororder_210621-Ibrahim01-Talks to revive Iran nuclear agreement

Mataimakin babban sakatare kana darektan harkokin siyasa a kungiyar Tarayyar Turai (EU) Enrique Mora, ya sanar a jiya Lahadi cewa, an kusa cimma matsaya a tattaunawar da ake yi game da farfado da cikakkiyar yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran (JCPOA), bayan ganawa ta baya-bayan da ta kai ga kawo karshen zagaye na shida na tattaunawar sassantawa da aka yi a baya.

Mora ya shaidawa manema labarai bayan ganawar hukumar hadin gwiwar yarjejeniyar ta JCPOA, wadda ta samu halartar wakilai daga kasashen Sin da Faransa da Jamus, da Rasha da Burtaniya da Iran cewa, “mun kusa kai ga cimma yarjejeniya, amma ba mu kai ga haka ba tukuna.

Dukkan mahalarta tattaunawar, za su koma kasashensu don kara tattaunawa. Ya ce, yana fatan a tattaunawa ta gaba, wakilan za su dawo da bayanai da, ra’ayoyi kan yadda za a kai ga cimma matsaya.”

Jami’in na EU ya lura da cewa, an gudanar da tattaunawar ta wannan karo ne, bayan muhimman ci gaban siyasar da aka samu, inda ya ba da misali da tattaunawar baya-bayan da aka yi tsakanin babban wakilin EU mai kula da harkokin kasashen waje da manufofin tsaro Josep Borrell da jami’an Amurka a taron kolin EU da Amurka, da kuma ganawar da Borrell ya yi da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammed Javad Zarif. (Ibrahim Yaya)