logo

HAUSA

Sinawa Sama Da Biliyan Guda Sun Karbi Riga-kafin COVID-19

2021-06-21 18:36:07 CRI

Sinawa Sama Da Biliyan Guda Sun Karbi Riga-kafin COVID-19_fororder_A

Masu hikimar magana na cewa, “yabon ya zama dole.” Yayin da mahukuntan kasar Sin suka tsaya tsayin daka wajen tabbatar da yiwa al’ummar kasar riga-kafin cutar COVID-19, za mu iya cewa wannan batu ya dauki hankalin al’ummun kasa da kasa bisa yadda kasar ta himmatu domin sauke muhimmin nauyin dake bisa wuyanta na yiwa al’ummar Sinawa riga-kafin COVID-19. Kawo yanzu dai tafiya ta yi matukar nisa a ayyukan riga-kafin da kasar ke yi duk da kasancewarta a matsayin kasar dake sahun gaba a duniya ta fuskar yawan al’umma. A halin yanzu yawan riga-kafin da kasar ta yiwa jama’arta ya kai kashi daya bisa uku na jimillar riga-kafin COVID-19 da aka gudanar a duniya baki daya. Dama dai masu hikimar magana da cewa, “da zafi-zafi a kan budi karfe.”

A bisa ga bayanan da hukumomin lafiyar kasar Sin suka bayyana ya nuna cewa, ya zuwa ranar 19 ga watan Yunin shekarar 2021, larduna 31 da yankuna masu cin gashin kansu da biranen kasar dake karkashin ikon babban yankin gwamnatin kasar da rukunin sojoji ma’aikata masu ba da taimako a jihar Xinjiang sun ba da rahoton cewa, jimillar alluran riga kafin COVID-19 da aka yiwa al’ummun Sinawa sun zarce biliyan 1 a halin yanzu, hakan shi ke tabbatar da cewa kasar Sin tana matsayin farko ta fuskar yawan riga-kafin da aka yi da kuma yawan al’ummun kasar da aka yiwa riga-kafin. A sa'i daya kuma, shirin yiwa Sinawa mazauna kasashen ketare riga-kafin kawo yanzu an yiwa Sinawa sama da miliyan 1 alluran riga-kafin COVID-19 dake kasashe da yankunan duniya fiye da 150. Koda yake, kokarin da kasar Sin ke yi bai takaita kan kiyaye tsaro da lafiyar 'yan kasar kadai ba, har ma kasar tana kara mayar da hankali sosai kan kiyaye lafiyar 'yan kasashen waje da ke kasarta.

A halin yanzu, yankuna da dama a kasar Sin sun shigar da 'yan kasashen waje cikin shirin ayyukan riga-kafin annobar da tsarin aiki na yankunan unguwanni don ba da tabbaci ga biyan bukatunsu yadda ya kamata. Kawo yanzu dai aikin bincike da bunkasa ayyukan alluran riga-kafin COVID-19 na kasar Sin yana matakin farko a duniya, kuma kasar Sin tana tsayawa tsayin daka a sahun farko wajen hadin gwiwa da kasa da kasa game da shirin samar da allurar riga-kafin cutar. Bugu da kari, kasar Sin tana ba da tallafin riga-kafin ga kasashe masu tasowa dake da bukata cikin gaggawa da sojojin kiyaye zaman lafiya daga kasashe daban daban. Bayanai daga ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin sun nuna cewa, ya zuwa farkon watan Yuni, kasar Sin ta riga ta fitar da alluran riga-kafin zuwa kasashe sama da 40. Tana kuma taka muhimmiyar rawa a cikin shirin "COVAX” na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya zuwa yanzu dai, ta riga ta kammala rukunin farko na aikin alluran rigakafin a hukumance. (Ahmad Fagam)