logo

HAUSA

An tabbatar da burin kyautata tsarin aikin gona a taron FAO

2021-06-21 11:59:20 CMG

An tabbatar da burin kyautata tsarin aikin gona a taron FAO_fororder_hatsi

Daga ranar 14 zuwa ta 18 ga wata ne, aka gudanar da taron hukumar abinci da aikin gona ta MDD (FAO) karo na 42 a Rome na kasar Italiya, inda aka tantance tsarin da hukumar za ta yi amfani da shi wajen aiwatar da ayyukanta cikin shekaru 10 masu zuwa.

Taron na wannan karo, shi ne irinsa na farko da aka gudanar ta kafar bidiyo, inda wakilai fiye da 1300 suka halarci zaman, ciki har da ministoci da mataimakansu 119. A yayin bikin bude taron, babban sakataren hukumar FAO Mista Qu Dongyu ya nanata muhimmancin kirkiro sabbin fasahohi a fannin aikin gona, ta la’akari da burin da MDD ta sanya na samun ci gaba mai dorewa, ya zuwa shekarar 2030.

“Annobar cutar COVID-19 ta haifar da mummunan tasiri kan tsarin samar da abinci ta aikin gona, da tsananta yanayin da wasu kasashe suke ciki na fama da matsalar karancin abinci. A ganina, dole ne hukumar FAO ta taimakawa mambobinta daidaita manufofi, don ganin an cimma burin samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030. A yi kokarin tabbatar da makomar aikin gona ta hanyar raya kimiyya, da kirkiro sabbin fasahohi, da yin amfani da fasahar zamani mai alaka da na’ura mai kwakwalwa ta kamfuta.”

Kasar Italiya ita ce mai karbar bakuncin taron na wannan karo. Shugaban kasar Sergio Mattarella, a cikin nasa jawabi, ya yi bayani kan rawar da kasarsa ke takawa a kokarin farfado da aikin gona daga mummunan tasirin da cutar COVID-19 ta haifar, ya kuma bukaci kasashe daban daban da su kara kokarin daidaita matsalar karancin abinci a duniya. A cewarsa,

“Annobar cutar COVID-19 ta hana manoma zuwa gonakinsu, gami da haifar da matsala ga ayyukan gyara tsarin aiki, da zirga-zirga, da jigilar kayayyaki, da gurgunta manufofinmu na dora cikakken muhimmanci kan raya aikin gona. A wannan hukumar da muke ciki, wadda ta kunshi kasashe daban daban, ya kamata mu bullo da wasu dabaru masu alaka da bangarorin duniya daban daban, wadanda suka cimma matsaya a kai.”

A nasa bangare, Mista Tang Renjian, minista mai kula da aikin gona da harkokin kauyuka na kasar Sin, ya yi jawabi a wajen taron babbar muhawara kakarshin zaman hukumar FAO na wannan karo cewa, aikin daidaita tsare-tsaren samar da abinci ta aikin gona na bukatar hadin gwiwar kasashe daban daban. Saboda haka kasar Sin ta yi kira da a kara musayar ra’ayi tsakanin kasashen, don tabbatar da samun karin ra’ayoyi na bai daya. Ban da wannan kuma, ya kamata a kara kokarin kirkiro sabbin fasahohi, tare da hada aikin gona da kimiyya da fasaha a waje guda, da inganta aikin ciniki, don tabbatar da moriyar bai daya. Mista Tang ya kara da cewa,

“Kasar Sin ita ce kasa mafi girma a cikin kasashe masu tasowa, kana babbar kasa ce dake kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta. Tana son yin kokari tare da sauran mambobin hukumar FAO, don cimma burin samun ci gaba mai dorewa cikin sauri. Haka zalika, kasar na son ba da gudunmawa ga aikin kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.”

Taron hukumar FAO, taro ne dake jagora ga tsarin kungiyar, wanda a kan gudanar da shi duk shekaru biyu-biyu. A yayin taron ne kuma, ake tabbatar da manufofin hukumar, da zartas da kasafin kudinta, gami da ba da shawara ga kasashe mambobi, musamman ma a fannonin aikin samar da hatsi, da aikin gona. A yayin taro na wannan karo, an zartas da tsare-tsaren aiki na hukumar na shekarar 2022 zuwa 2023, da na shekarar 2022 zuwa 2025, gami da babban tsarin aiki na shekarar 2022 zuwa ta 2031, don neman kyautata yanayin aiki na hukumar. (Bello Wang)

Bello