logo

HAUSA

Raisi ya lashe zaben shugabancin Iran

2021-06-20 17:06:51 CRI

Raisi ya lashe zaben shugabancin Iran_fororder_7af40ad162d9f2d3994bf9fc68e2251b6327cc67

Babban jami’in hukumar shara’a, Ebrahim Raisi, ya lashe zaben shugabancin kasar Iran inda ya samu sama da kashi 60 bisa 100 na yawan kuri’un da aka jefa, ma’aikatar cikin gidan Iran ta bayyana hakan.

Tun da farko a wannan rana, shugaban kasar Iran mai barin gado Hassan Rouhani, ya ziyarci zababben shugaban kasar a ofishinsa kana ya taya shi murnar lashe zaben.

Rouhani ya bayyana a taron manema labarai cewa, yayin da Raisi zai kama aiki a ranar 4 ga watan Augasta, zai kasance a matsayin shugaban kasa ga dukkan jama’ar kasar, kuma dukkan jama’ar kasa zasu goya masa baya shi da gwamnatinsa.

Rouhani ya bayar da cikakken hadin kansa da na majalisar ministocinsa  ga mutumin da zai gaje shi, domin a tabbatar da samun nasarar mika mulki ga sabuwar gwamnatin kasar.

Masu sharhi kan al’amurra sun bayyana cewa, Raisi ya samu goyon bayan al’ummar kasar ne sakamakon fatan da suke da shi a gare shi na ganin ya inganta yanayin tattalin arzikin kasar wanda ya gamu da mummunan koma baya sakamakon takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran da kuma yanayin da aka shiga sakamakon tasirin annobar COVID-19.

Game da batun hulda da kasashen ketare kuwa, Raisi ya sanar da cewa, zai bayar da fifiko kan batun hadin gwiwa da yin cudanya da kasashen duniya.(Ahmad)