logo

HAUSA

Kafar yada labaran Amurka: Riga-kafin Sin ya taimakawa kasashe masu tasowa wajen rage bala’in COVID-19

2021-06-19 16:31:08 CMG

Kafar yada labaran Amurka: Riga-kafin Sin ya taimakawa kasashe masu tasowa wajen rage bala’in COVID-19_fororder_0619-alluran rigakafi-Ahmad

Jaridar Wall Street Journal ta kasar Amurka, ta wallafa rahoto a farkon wannan mako dake nuna cewa, riga-kafin kasar Sin ya taimakawa kasashe masu tasowa a nahiyar Asiya wajen rage wahalhalun samun riga-kafin annobar COVID-19.

A cewar rahoton, kasar Indonesia ta dogara ne kacokan kan riga-kafin da kamfanin Sinovac Biotech ya samar, yayin da kasar Cambodia ta yi gagarumin amfani da riga-kafi nau’i biyu wanda kasar Sin ta samar, hakan ya bata nasarar kasancewa kasar da tafi kowace kasa a shiyyar gudanar da ayyukan riga-kafin, kasar Philippines tana sa ran samun karin alluran riga-kafin wanda ake tsammanin za su isa kasar a wannan wata, sama da kashi 50 bisa 100 na riga-kafin kasar wanda Sin ta samar ne.

Evan Laksmana, wani babban mai nazari a cibiyar tsara dabaru da nazarin kasa da kasa dake Indonesiya, an rawaito yana fadin cewa, mazauna shiyyar zasu iya tuna yadda kasar Sin ta gaggauta kafa dokar kulle, inda ta samu nasarar dakile bazuwar cutar kana ta samar da riga-kafi.

Jaridar ta bayyana cewa, riga-kafin kasar Sin ya kasance a matsayin wanda ya taimakawa biyan bukata a kudancin Asiya, yayin da kasashen da ma suka fi mayar da hankali kan riga-kafin kamfanin AstraZeneca wanda kasar Indiya take samarwa, amma sakamakon tsananin yaduwar cutar COVID-19 a kasar ya haifar da katsewar ayyukan samar da riga-kafin.(Ahmad)

Ahmad