logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin zai ci gaba da ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya

2021-06-16 21:38:46 CRI

Tattalin arzikin Sin zai ci gaba da ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya_fororder_sin

Kwanan baya wani masanin tattalin arziki ya gayawa kamfanin dillacin labarai na Amurka na Bloomberg cewa, “Alkaluman tattalin arzikin kasar Sin zai kara habaka a fannin samarwa da bukatar kayayyaki,.” A yau Laraba alkaluman tattalin arzikin da gwamnatin kasar Sin ta fitar sun shaida wannan hasashe.

Hakika sakamakon da kasar Sin ta samu ya danganta da kokarin da gwamnatin kasar da kamfanonin kasar da kuma al’ummun Sinawa suka yi, an lura cewa, tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, manufofin da kasar Sin take aiwatarwa bisa manyan tsare-tsare sun dace da yanayin da kasar ke ciki wato sun taimaka matuka wajen daidaita matsalolin da kamfanonin kasar ke fuskanta, a sa’i daya kuma, kasar Sin tana himmatuwa kan aikin kirkire-kirkire, tare kuma da kara biyan bukatu a cikin gida, ta yadda za a ciyar da tattalin arziki yadda ya kamata.

A bisa wannan yanayi, ana hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun farfadowa, hakika sabon rahoton da bankin duniya ya fitar ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai taka babbar rawa kan karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2021 da muke ciki, inda zai kai kaso 25 bisa dari.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)