logo

HAUSA

Amurka Ba Ta Cancanci Zama Abun Koyi A Fannin Kare Hakkin Bil Adama Ba

2021-06-16 15:29:42 CRI

Amurka Ba Ta Cancanci Zama Abun Koyi A Fannin Kare Hakkin Bil Adama Ba Saboda Tarihin Ta Na Kisan Gillar Al’Ummun Amurka Masu Asali Daga India_fororder_15323999091

Daga Amina Xu

 

Kwanan nan, jaridar “The Guardian” da “The Punch”, sun ruwaito labaran da kafofin yada labarai na Amurka suka wallafa, masu nasaba da wani nazarin da aka yi kan yankin Xinjiang, inda aka yi zargin cewa, Sin ta yiwa ‘yan kabilar Uygur kisan gilla, a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, wai kuma har adadin jarirai da matan Uygur suka haifar ya ragu da kashi 84%

Wadannan jaridu ba su san hakikanin hali da ake ciki a yankin ba, domin kuwa hukumar kididdigar ta jihar Xinjiang ta fidda alkaluma a ranar 14 ga wata, inda ta karya wannan zargi. Alkaluma na nuna cewa, ya zuwa ran 1 ga watan Nuwamba shekarar 2020, yawan mutanen jihar ya kai 25,852,345, wanda ya karu da kashi 18.52% bisa alkaluman da aka samar a shekarar 2010, wato yawan karuwa da aka samu a ko wace shekara ya kai 1.71%.Alkaluman da suka haura na kasar Sin baki daya da kaso 13.14% da 1.18%.

Idan an kwatanta da kididdigar da aka yi a shekarar 2010, yawan al’ummar kananan kabilun jihar ya karu da mutum 1,865,061, adadin da ya karu da kashi 14.27%, a yayin da alkaluman karuwar kananan kabilu a duk fadin kasar ya kai kaso 10.26% ne kacal. Daga cikinsu kuma, yawan ‘yan kabilar Uygur ya kai 11,624,257, adadin da ya kai kaso 44.96% na yawan al’ummar jihar baki daya.

Alkaluman sun kuma nuna cewa, yankin na samun bunkasuwar tattalin arziki da al’umma a shekarun baya-baya nan, wanda hakan ya jawo jari daga waje, matakin da ya ingiza karuwar yawan mutane. Abin da ya shaida cewa, al’ummun yanki na samun ci gaba sosai karkashin jagorancin jam’iyyar JKS.

Amurka a idanun wasu kasashe, na matsayin “Abun misali game da kare hakkin Bil Adama” wadda kuma ta sha tsoma baki kan harkokin kare Bil Adama a yankin Xinjiang. To amma shin ko Amurkan na tafiyar da aikin kare hakkin Bil Adama yadda ya kamata a cikin kasar ta?

Sanin owa ne Red Indians sun kasance ainihin mazauna nahiyar Amurka ta arewa , amma ‘yan mulkin mallaka fararen fata sun kashe su kamar su dabobbi ne. Ya zuwa karshen karni na 19, yawansu ya ragu zuwa dubu 250. Kuma tun da Amurka ta kafa kasarta zuwa farkon karni na 20, wadannan al’ummu sun rasa yawancin filayensu. Ban da wannan kuma, an tilastawa yaransu su bari iyalansu, da hana su amfani da harshensu, yayin da wasu ma ba su ko san asalinsu ba ko kadan.

Filayen da gwamnati ta baiwaainihin mazauna kasar, dukkansu a wurare ne mafi talauci, ko marasa ni’ima, kamar su tsaunuka da hamada. Amurka tana kokarin kwace makamashi da dukiyoyi daga hannun sauran al’ummu, don raya kanta, har ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya. Tarihinta mai kunshe da rashin imani abu ne da ba za a manta da shi ba.

Don haka irin wannan kasa, ba ta cancanci ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, bisa hujja ta wai demukuradiyya da kare hakkin Bil Adama.

Ban da tarihinsu mai ban tausayi, halin da ainihin mazauna kasar ta Amurka suke ciki yanzu ma ba shi da kyau ko kadan. ‘Yan Navajo na daga cikin ainihin mazauna wannan shiyya, sai da har yanzu yawansu da ya kai kaso 30% ba su samun wutar lantarki, kana kaso 40% ba su da ruwan famfo. Tun barkewar cutar COVID-19 a shekarar 2020, yankin ‘yan kabila da ya dade yana fuskantar kalubale mai tsanani, har ya zama wurin da aka fi samun yawan masu harbuwa da cutar da kuma mamata sakamakon cutar.

Ainihin mazauna kasar Amurka, ciki hadda Navajo sun dade suna rayuwa a wannan nahiyar har fiye da shekaru dubu 10, amma yanzu suna cikin mawuyancin hali.

A yayin da ainihin mazauna kasar Amurka suke rayuwa maras dadi, a hannu guda kuma, yankin Xinjiang na samun bunkasuwa cikin wadata, abun da ya karyata karairayin da Amurka take yi kan Xinjiang, cewa wai ana yiwa ‘yan kabilar Uygur kisan gilla, da keta hakkin Bil Adama.

Kamata ya yi ‘yan amshin shatan Amurka su farka, su gane cewa wadannan karairayi ba za su kawar da hankalin mutane ba. Laifi tudu ne, ka take naka ka hango na wani.Tarihin kisan gillar da aka yi wa ‘yan asalin kasar Amurka na nuna cewa, Amurka na fakewa da batun kabila da kuma kare hakkin Bil Adama, don kalubalantar kasar Sin, domin ita ce ta taba yin hakan. Don haka ya kamata Amurka ta warware matsalarta a wannan fanni da farko, kafin ta tsoma baki cikin harkokin yankin Xinjiang. (Amina Xu)