Mahakar gishiri da ake amfani da ita wajen warkar da masu ciwon huhu
2021-06-10 14:52:48 CRI
Wannan wata mahakar gishiri ce ta karkashin kasa mai zurfin mita 135 dake kasar Poland, wadda ake amfani da ita wajen warkar da masu ciwon huhu. A matsayin daya daga cikin mahakar gishiri mafi dogon tarihi a duniya, hukumar UNESCO ta shigar da wannan mahakar gishirin cikin jerin wuraren tarihi na duniya.