logo

HAUSA

Ziyarar Fa’iza a birnin Shanghai na kasar Sin

2021-06-09 10:24:50 CRI

A kwanakin baya ne, abokiyar aikinmu Fa’iza Mohammed Mustapha ta ziyarci birnin Shanghai na kasar Sin, a wani bangare na ziyarar aikin da tawagar ma’aikatan sassa daban-daban dake aiki a babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) yake kaiwa sassan kasar Sin, don dauko rahotanni game da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannoni daban-daban, kamar yaki da talauci, raya yankunan karkaka, ababan more rayuwa da sauransu.

Ziyarar Fa’iza a birnin Shanghai na kasar Sin_fororder_20210609世界21021-hoto2

Wuraren da suka ziyararta a Shanghai a wannan karo, sun hada da jami’ar koyar da harkokin wasanni, inda ake koyar da dalibai fasahohin wasanni kala-kala, kamar kwallon kafa da kwallon tebur, kwallon Kwando da na gora da wasan ’yar giya da sauran wasanni, har ma daga bisani irin wadannan dalibai su kware a matsayin masu horas da wasanni.

Sauran wuraren da suka kai ziyara sun hada da dakin cin abincin makarantar inda suka ganewa idonsu tare da dandana nau’o’in abincin da ake sayarwa da tsarin sayar da abinci, da wani Titin hada-hadar saye da sayarwa dake alamta birnin Shanghai na kasar Sin, da sauransu.

Ziyarar Fa’iza a birnin Shanghai na kasar Sin_fororder_20210609世界21021-hoto3

Tawagar ta kuma ziyarci wani masallaci mai dogon tarihi a birnin na Shanghai, abin da ke kara karyata jita-jitar da wasu kasashen yamma ke yayatawa, wai babu ’yancin bin addini a kasar Sin. (Fa’iza, Ibrahim/ Sanusi Chen)