logo

HAUSA

Gasar birnin Beijing za ta zama cikar burin Olympic na lokacin hunturu

2021-06-07 10:55:56 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa IOC Mr. Thomas Bach, a ranar 7 ga watan nan na Mayu, inda ya taya Mr. Bach din murnar sake zabarsa a matsayin shugaban kwamitin na IOC.

Kaza lika shugaba Xi ya jaddada muhimmancin kasacewar gasar Olympics, da ta ajin nakassu da birnin Beijing zai karbi bakunci, a matsayin babban dandali ga dukkanin kasashen duniya, wanda zai ba da damar gudanar da gasa bisa adalci tsakanin ‘yan wasan kasa da kasa.

Hakika kwamitin IOC ya cancanci yabo, duba da yadda ya yi matukar kokari wajen goyon baya, da ba da jagoranci wajen cimma nasarar shirya gasar Olympics da ta nakasassu, wadda birnin Beijing zai karbi bakunci a badi. Kasar Sin na cike da kyakkyawan fata na gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing kamar yadda aka tsara. Kaza lika Sin na fatan ci gaba da aiki tare da kwamitin IOC, da sauran sassan kasa da kasa wajen tabbatar da nasarar wannan gasa cikin sauki, kuma tare da tsaron lafiya da nishadantarwa.

Shekaru 6 da suka gabata, cikin birane 5 da suka fara neman karbar bakuncin gasar hunturu ta shekarar 2022, wasu sun janye bukatar ta su bisa radin kan su, sakamakon wasu kalubale na siyasa a cikin gida, wasu kuma sun dakatar da bukatar su saboda gwamnatocin su, sun gaza samar da tallafin kudi da suke bukata, yayin da birane Beijing da Zhangjiakou suka samu goyon baya daga daukacin al’ummar Sinawa. Bayan nazari, tawagar kwamitin Olympic sun ziyarci wurare a sassan kasar Sin, sun yi bincike cikakke, an kuma yi mahawara sosai tare da kwamitin shirya gasar Olympic na Beijing, kafin a mika ikon karbar bakuncin gasar ga biranen Beijing da Zhangjiakou.

Sakamakon haka, birnin Beijing ya zama birni na farko a duniya, wanda zai karbi bakuncin gasar Olympics ta lokacin zafi, da ta lokacin hunturu da kasar nahiyar Asiya. Kaza lika birnin Zhangjiakou tare da Beijing, sun kasance na farko a Sin, da suka yi nasarar karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin hunturu.

Tun daga wannan lokaci ne kuma, Sin ta shiga aiki ba dare ba rana, don samar da dukkanin kayayyakin da ake bukata na filaye, na’urori da kayan aiki, ta yadda za a kai ga gudanar da wannan gasa ta Olympics da ta nakasassu ta lokacin zafi cikin nasar. A yau, Dukkanin wuraren da za a yi wannan gasa sun kammala, an tsara komai an shirya duk ayyuka cikin tsanaki, an tanaji dukkanin hidimomi a kan lokaci, kana an shirya yadda za a watsa shirye shirye da bukukuwan al’adu cikin tsanaki. Kari kan hakan, Sin ta kuma gudanar da gwajin wasannin kankara da na dusar kankara, domin gwada muhimman bangarorin da ake bukata yayin gasar, yayin da a watanni 6 na karshen shekarar nan ma, za a samar da Karin damammaki na yin hakan. Ko shakka ba bu, alkawarin gudanar da gasar Olympics da Beijing zai karbi bakunci, zai cika ba tare da wata matsala ba.

Ana kallon wannan gasa ta lokacin hunturu da za ta kasance karo 24 a tarihin gasar Olympics ta hunturu a shekarar 2022, a matsayin gasar da za ta gudana a wata gaba ta tarihi, wato lokacin da zai yi daidai da fara aiwatar da shirin bunkasa kasar Sin na shekaru biyar biyar karo 14. Lokaci ne na nunawa duniya kimar kasar Sin a fannin bunkasar da ta samu. Kana wata dama ce mai muhimmanci ta ingiza kimar kasar. Tuni kuma shugaban kasar Xi Jinping ya jaddada muhimmancin hakan. In da a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2016, ya jagoranci wani taro a Zhongnanhai, inda ya saurari rahoto game da shirin da ake yi, na gudanar da gasar Olympics da ta nakasassu ta lokacin hunturu wadda birnin Beijing zai karbi bakunci. A lokacin shugaban na Sin ya jaddada cewa, abu ne mai muhimmanci, kuma nauyi ne kan kasar Sin ta gudanar da wannan gasa cikin nasara. Ya yi fatan za a gudanar da gasa mai kayatarwa, wadda ta zarce makamantan ta da suka gabata. Kana ta zama gamsasshiyar amsa ga ‘yan kasa da ma baki na kasa da kasa da za su halarta.

A watan Janairun bana, shugaba Xi Jinping ya yi ran gadi a Beijing da Hebei, ya kuma shugabanci tarukan sauraron halin da ake ciki, game da shirin gasar Olympics ta masu lafiya da masu bukatar musamman ta Beijing ta 2022, inda ya yi nuni da cewa, gina wani karfi na raya wasanni muhimmin tubali ne, na samar da al’ummar gurguzu ta zamani a dukkanin fannoni. Abu ne a zahiri, wasanni suna ci gaba da baiwa rayuwar dan adam fa’ida, kuma tasirin wasanni sun kasance alama ta zahiri wadda ke shaida kimar farfadowar kasar Sin.

Ana kallon gasar Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing zai gudanar a badi, a matsayin aiki mai kima matuka saboda dalilai kamar haka:

Da farko, gasar hunturu ta birnin Beijing za ta yayata ci gaban da kasar ta samu, a fannin raya wasannin lokacin sanyi da na dusar kankara. A hannu guda kuma, muhimmin ci gaba ne a fannin raya yankin Beijing zuwa Tianjin zuwa Hebei. Har ila yau, kammala aikin layin dogo na Beijing zuwa Zhangjiakou, da Beijing zuwa Lijiazhuang sun kasance jigon shirya ayyukan gasar dake tafe, wanda zai hade yankunan Zhangjiakou, da Chongli, da Yanqing da birnin Beijing zuwa layi guda, yayin da yankin Yanqing da Zhangjiakou a hukumance, suka shiga tsarin birni guda da za a iya ziyarta cikin sa’a daya, kana ana iya kewaya zirin raya al’adun yawon bude ido da zai hade sassa da birnin Beijing zuwa Zhangjiakou, zai kuma sanya wani sabon kuzari na raya yankin Beijing zuwa Tianjin zuwa Hebei.

Karkashin wannan gasar ta lokacin hunturu, yankin Chongli, wanda a baya ba shi da karfin tattalin arziki, a yanzu ya samu manyan sauye sauye. A yanzu haka duk cikin mutum 4 dake wannan yanki, daya na wani aiki mai nasaba da wasan kankara ko dusar kankara. Da yawa daga al’ummar Chongli, wadanda suka jima suna aiki a wajen yankin, a yanzu sun koma gida. Ko shakka babu wannan harka ta raya wasannin kankara ta kawo babban sauyi ga al’ummar wadannan gundumomi.

Abu na biyu, karbar bakuncin gasar Olympics da ta nakasassu za su taimaka wajen kara yayata wasannin kankara da na dusar kankara a Sin. Cikin bangarorin ayyuka 109 da za a gudanar karkashin wannan gasa ta Olympics ta birnin Beijing, 1 bisa 3 an gudanar da su ne a wajen kasar Sin. A hannu guda kwamitin shirya wannan gasa ta Olympics na birnin Beijing, ya taimakawa tawagogin kasashe daban daban, wajen samun horo, da sauran kananan ayyuka masu nasaba da gasar. Ana iya cewa, wannan gasa ta birnin Beijing ta samar da kyakkyawar dama ga Sin ta cike wasu gibi, da karfafa fannin wasanni. Baya ga ‘yan wasan kasar Sin da a baya suka taba lashe lambobin yabo, wadanda a yanzu za su samu damar shiga a dama da su wasannin kankara, a daya hannun, hakan zai ba da zarafi na karfafa wasanni da a baya ba a ba su muhimmanci, ta yadda za su shiga gasanni na wasa yadda ya kamata.

Gasa ce da za ta kara sauri, da karfi, da ingancin wasannin kasar Sin. A lokaci guda kuma, gasar za ta ingiza sha’awar karin mutane a fannin nuna kauna, da shiga harkokin wasannin hunturu, hakan zai kuma cika burin Sinawa kusan miliyan 300 na shiga wasannin hunturu, zai kuma sauya matsayin wasannin kankara a Sin, tare da fadada hakan daga yankunan arewaci zuwa kudancin kasar, daga yammaci har gabashi.

Ko shakka babu, kudurorin raya wasannin hunturu na gwamnatin kasar Sin, sun ingiza sha’awar karin mutane, ta yadda za su shiga wasannin kankara, tare da kara hade sassan masana’antun dake da nasaba da wasan na hunturu, kana hakan zai hade karin sassan wasannin motsa jiki da kasar ke da su da na kankara, da hade sassan wasannin motsa jiki da fannonin inganta lafiyar al’umma, tare da agazawa mutane, ta yadda za su zama masu karfin tasiri a fannin wasanni tun daga tushe.

Idan har wasanni suka samu tagomashi, Sin za ta kara karfi, kuma fannin wasannin kasar zai bunkasa. Wasanni wani karfi ne mai saukin aiwatarwa, wanda ke fayyace cigaban kasa. Idan an kalli kasar Sin ta can baya, za a ga kasa ce mai rauni da talauci, mutanenta sun yi fama da talauci da cututtuka. A can baya Liu Changchun ya halarci gasar Olympics shi kadai, ya kuma bar duniya da tunanin abun da ya faru. Sai dai a karshe,  shugabancin Jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin a sabon zamani, ya samar da amsa ga wadannan tambaya, wato "Tambayoyi 3 game da gasar Olympics". A yanzu, ya zama wajibi a shirya sosai, domin sauke nauyin dake wuyan Sin, na gudanar da gasar Olympics ta birnin Beijing, kana ana fatan shirya gasa mai kayatarwa, wadda ‘yan wasan hunturu na duniya za su shiga a dama da su yadda ya kamata, tare da cimma nasarar mafarkin gasar wasannin kankara, na Sin na kara farfadowar ci gaba.

Shugaban kwamitin kasa da kasa na shirya gasar Olympics Mr, Thomas Bach, ya yi imanin cewa, kasar Sin za ta nunawa duniya dabarar yaki da annoba, da hanyoyin inganta ci gaban wasannin kankara da dusar kankara, tare da samar da babbar gudummawa, wajen daga matsayin gasar. Hakan alama ce wadda ke tabbatar da ikon kasar Sin, na aiwatar da gasanni cikin karfin hali, tare da nunawa duniya kyakkyawan yanayin kasar.