logo

HAUSA

Abba Garba: Maida hankali kan raya kimiyya da fasaha ya sa kasar Sin ta samu babban ci gaba

2021-06-01 14:44:36 CRI

Abba Garba: Maida hankali kan raya kimiyya da fasaha ya sa kasar Sin ta samu babban ci gaba_fororder_微信图片_20210531224221

Abba Garba, dan Najeriya ne wanda a yanzu haka yake gab da kammala karatun digirinsa na uku a fannin na’ura mai kwakwalwa a jami’ar Peking dake kasar Sin, ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin tsarin karatu dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashe.

A cewarsa, duba da yadda gwamnatin kasar Sin take himmatuwa wajen zurfafa bincike da yin kirkire-kirkire a bangaren kimiyya da fasaha, da yadda take darajanta masana kimiyya gami da karfafawa al’umma gwiwar karo ilimi, ya sa kasar ta samu babban ci gaba.

A karshe, malam Abba Garba ya kuma yi kira da a karfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, a fannin raya harkokin kimiyya da fasaha. (Murtala Zhang)