logo

HAUSA

Shugaban hukumar CFA ya bayyana fatan ganin kungiyar Sin ta samu gurbin buga gasar cin kofin duniya ta 2022

2021-05-27 12:21:26 CRI

Shugaban hukumar CFA ya bayyana fatan ganin kungiyar Sin ta samu gurbin buga gasar cin kofin duniya ta 2022_fororder_0527-wasanni

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Sin ta CFA Chen Xuyuan, ya sha alwashin kai kungiyar Sin ta maza, zuwa matsayin samun gurbin buga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 daga rukunin kasashen nahiyar Asiya.

Shugaban hukumar ta CFA ya ce, ‘yan wasan Sin za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da sun cimma nasarar samun gurbin buga gasar da hukumar FIFA ke shiryawa. Wadda a shekarar ta badi za ta gudana a kasar Qatar.

Kungiyar kwallon kafar Sin za ta buga wasannin ta na neman gurbin ne tare da kasashen Guam, da Maldives, da Philippines, da kuma Syria, a wasannin rukunin A, wasannin da tuni aka tsara gudanar da su a birnin Suzhou daga ranar 30 ga watan Mayun nan, zuwa 15 ga watan Yunin dake tafe.

Duk da cewa a yanzu Sin na da maki 8 ne, kasa da Syria, wadda ke jagorantar rukunin. Kuma tana gaban Philippines ne kadai bisa banbancin yawan kwallaye, shugaban na CFA ya ce yana da kwarin gwiwar ganin tawagar ta kai ga cimma burin ta na samun gurbi.

Ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bai ga dalilin da zai haka Sin kaiwa ga nasara ba. Ya ce "Da farko, kungiyar Sin na da karfi na kaiwa ga samun gurbin da take nema. Na biyu kuma, ‘yan wasan ta sun samu horo na tsawon sama da shekara bisa burin da suka sanya gaba. Kaza lika masu horas da ‘yan wasan kasar sun koyi darussa daga rashin nasarar da suka samu a baya. Har ila yau, CFA na aiki tare da tawagar kasar Sin, wajen samar da dukkanin damar da ake bukata bisa kwarewa, domin cimma wannan buri".

Ya kara da cewa "Mun dade muna fatan baiwa al’umma damar ganin ci gaba da kwallon kafar kasar Sin ta samu. Amma idan aka cire mu daga wannan mataki na neman gurbin buga gasar cin kofin duniya, wasu na iya kallon hakan a matsayin alamar koma bayan mu, maimakon ci gaba".

Akwai kungiyoyi 40 da aka raba su zuwa rukunoni 8 a wannan mataki na neman gurbi. Wadanda suka yi nasara za su wuce zuwa zagaye na karshe, kana 4 dake biye da su ma, za su samu gurbin buga gasar ta cin kofin duniya.

Bisa sakamakon da ke hannu a yanzu, ya zama wajibi Sin ta kaucewa rashin nasara, ko kunnen doki a ragowar wasanni 4 da za ta buga, in ba haka ba kuwa, za ta iya rasa damar gurbin da take son samu.

Game da haka, Chen ya ce "Na shiryawa wasannin, kuma ina da kwarin gwiwar cewa ‘yan wasan mu za su yi rawar gani". Ya kara da cewa, CFA ta ware kudin kyauta har RMB miliyan 12, kimanin dalar Amurka miliyan 1.8, domin karfafar gwiwar ‘yan wasan na Sin.

Ya ce "Kudi ne masu yawa. Ina ga sun isa su karfafa gwiwa".

Masharhanta dai na ganin cewa, rashin mayar da hankali ga horas da ‘yan wasan kwallon kafa a gida, da rashin shigar Sinawa da yawa cikin wasan kwallon kafa ne ya haifar da koma bayan da wasan ke fuskanta a kasar.

Game da hakan, Chen ya ce CFA za ta kara azama wajen ganowa, da horas da matasa masu basira, ta yadda za su kai ga wakiltar kasar Sin a nan gaba. Hakan ya sa a bana za a bude gasar kwallon kafa ta matasa a duk fadin kasar Sin, wadda za ta hade daukacin ‘yan wasan kwallon kwalejoji da cibiyoyin ilimi na kasar.

A daya bangaren kuma, za a kafa wani sansani na dindindin, domin horas da rukunonin ‘yan wasan kwallo a sassan kasar Sin, matakin da ake sa ran zai baiwa matasa damar samun horo akai akai, maimakon irin sansanonin dake gudana a kankanen lokaci a yanzu.

Kari kan haka, CFA za ta yi aikin zabo matasa masu basira domin aika su sassan kasashen waje su samu horo da gogewa. Chen Xuyuan ya ce, "Manufar mu ita ce tura wani kaso na matasa zuwa kasashen ketare, domin su samo horo da kwarewa nan da shekara 1 zuwa 2 masu zuwa".

Ya ce “Batun raya matasa abu ne na yau da kuma gobe, don haka batun ko Sin za ta baiwa duniya mamaki a fannin ci gaban kwallon kafa, ya dogara ne ga yadda muka reni sabbin jini a yanzu."

Gasar ajin kwararru ta kasa

A wasan kungiyoyi ajin kwararru na kasar Sin, a karon farko kungiyar Jiangsu Suning ta yi nasarar lashe kambin gasar, bayan da ta doke Guangzhou Evergrande a wasan karshe da ya gudana cikin watan Nuwamba. Sai dai kuma, a karshen watan Fabarairun bana, mamallakan kungiyar mai mazauni a birnin Nanjing, sun ce sun janye kudaden gudanarwar ta, bayan da Suning FC din ta gaza samun mai zuba jarin da zai dauke bashin da ake bin ta, lamarin da ya sanya ta rasa damar shiga jerin kungiyoyin da za su taka leda a kakar wasa mai zuwa.

Da yake tsokaci game da hakan, tsohon shugaban rukunin Shanghai International Port Group ko (SIPG), dake mallakar kungiyar Shanghai Port FC, Mr. Chen, ya ce ficewar Jiangsu FC daga kungiyoyin da za su taka leda a kakar wasa mai zuwa babban abun takaici ne, wanda ya haifar da zazzafar mahawara.

Ya ce "Cikin shekarun baya bayan nan, kwararrun kungiyoyin kwallon kafar kasar Sin sama da 10 ne suka fuskanci irin wannan matsala ta fita daga jerin kungiyoyi masu lasisin buga gasar zakarun kungiyoyin kasar. Ya kuma aza tambayar cewa, ko mene ne dalilin yawaitar janyewar wadannan kungiyoyi? Kuma ta wadanne hanyoyi ne za a iya taimakawa kulaflikan da ma ita kan ta gasar, ta yadda za a samu dorewar tsarin gudanar da su cikin lumana?

A cewar sa, wadannan ne muhimman batutuwa da hukumar CFA ke aiki tukuru a kan su. Kaza lika ya bayyana cewa, fadada damar mallakar kungiyoyin kwallon kafar kasar, zai taimaka matuka wajen warware wannan matsala. Ya ce mutum guda, ya mallaki kungiya na iya zama sanadin durkushewarta, saboda nauyin jagoranci da daukar nauyin kungiyar baki daya ya rataya a wuyansa, yayin da idan mutane da dama ne ke mallakar kungiya daya, tare da tsarin kasuwanci da zai rika samun kulawar hukumar gudanarwa, mai kunshe da daraktoci, hakan zai taimaka wajen cimma matsaya, da yanke muhimman shawarwari, kamar batun ficewar kungiya daga buga gasa, wanda batu ne da ya dace hukumar gudanarwa ta yanke shawara a kai.

Baya ga shawarar fadada mallakar kungiyoyin, tuni hukumar CFA ta bullo da sabbin ka’idojin dakile wasu matakai marasa dorewa, da kungiyoyin ke aiwatarwa wajen tafiyar da harkokin su a kasar ta Sin, mafi yawan al’umma a duniya.

Wadannan ka’idoji sun hada da takaita kashe kudi tsakanin kulaflika, da baiwa masu zuba jari damar shigar da kudade, da dakile aukuwar asara, da duba batun kudaden albashin ‘yan wasa. Ga misali, sabuwar dokar ta kayyade albashin yuan miliyan 5, wato kusan dalar Amurka 780,000 ga ‘yan wasa na gida a duk shekara, yayin da ‘yan wasan ketare ka iya karbar albashin euro miliyan 3, kwatankwacin yuan miliyan 23.49 a shekara, wanda hakan ya janyo ‘yan wasan ketare masu yawa, dake rububin zuwa taka leda a kasar Sin gabanin bude kakar wasa dake tafe.

Chen ya ce ko da yake wadannan ka’idoji suna sauya yanayin wasannin da ake bugawa na ajin kwararru, a karshe za su ma taimakawa sashen kwallon kasar Sin a dogon lokaci. Ya ce "wasu sassan wasanni ba laifi, amma a gani na, wasu masu sha’awar wasan kwallo ba sa gamsuwa da wasu fannoni. Manufofin mu ba su shafi manyan ‘yan wasa ba, maimakon haka za su taimaka ne wajen kawar da rashin tabbas, da wasan kwallon kafar kasar Sin ya fuskanta cikin shekarun baya bayan nan. Wadannan matsaloli za su kawo karshe komai dadewa, kuma hakan zai yi alfanu ga sashen kwallon kafar kasar Sin."

Chen ya kara da cewa, burin CFA shi ne kawar da kulaflikan kwallon kafar Sin daga dogaro kacokan kan kudade daga manyan ‘yan kasuwa, ta yadda za su karkata ga dogaro da hanyoyi mafiya dorewa, da amfani da kwarewa.

Ya ce "Burin mu shi ne kwararrun kulaflika su kai ga iya samun daidaito cikin shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa. Ta hanyar cimma matsayin dogaro da kai, da tabbatar da samar da riba ga masu zuba jari ne kadai, karin masu zuba jari za su yi sha’awar shiga a dama da su a fannin”.

A matsayin sa na shugaban CFA, Chen ya yi imanin cewa, mataki mai muhimmanci na kai kulaflikan ga nasara shi ne, kaddamar da walawalar kwallon kafa ta kasa baki daya, wanda hakan zai karfafi kudurin kawo sauyi a fannin kwallon kafar Sin da gwamnati ta tsara.

Chen ya ce “Bangarorin gwamnati masu ruwa da tsaki a wannan batu, sun yi aiki tukuru a fannin bincike kan hakan, tun daga shekarar 2015, ko da yake akwai sauran batutuwa da ba a kai ga warware su ba. Ga misali batun tsara dabarun kaucewa asara, da dakile shirya coge ko sayar da wasanni. Ba zan iya cewa ga ranar da za a kammala ba, amma ina fatan aikin samar da walawalar na tafe nan da dan lokaci."

Sakamakon barkewar cutar COVID-19, kaso 2 bisa 3 na gasar kwallon kafar ajin kwararru ta Sin ko CSL ta kakar shekarar 2020, an buga ta ne cikin tsauraran matakan kandagarkin yaduwar cutar, inda kuma ake sa ran buga wasannin kakar dake tafe a manyan birane biyu, wato Guangzhou dake kudanci, da birnin Suzhou na gabashin kasar Sin.

Chen ya ce "Muna da burin dawowa salon buga wasannin gida da waje, a zango na biyu na karshen shekarar bana. Amma hakan ya dogara ne ga yanayin da za a gamu da shi game da cutar COVID-19".