logo

HAUSA

Yadda musulmin kasar Sin suka gudanar da azumi da ma shagulgulan bikin karamar sallah

2021-05-14 19:46:33 CRI

Yadda musulmin kasar Sin suka gudanar da azumi da ma shagulgulan bikin karamar sallah_fororder_微信图片_20210514194358

Barka da sallah, Eid Mubarak!

A jiya Alhamis ne,  musulmin kasar Sin sama da miliyan 20, suka bi sahun daukacin musulmin duniya, wajen gudanar da Idin karamar sallah. Shin kun san yaya musulman kasar Sin suka gudanar da azumi, da ma shagulgulan bikin karamar sallah?

A shirinmu na yau, mun samu damar tattaunawa da malam Sama'ila Usman, dan jihar Yobe, a tarayyar Nijeriya, wanda kuma yanzu haka yake karatun digiri na uku a jami'ar Lanzhou, wato a birnin Lanzhou, hedkwatar lardin Gansu.

Lardin Gansu yana a arewa maso yammacin kasar Sin, kuma lardi ne da musulmi masu yawa ke rayuwa, musamman ma ‘yan kabilar Hui, da Dongxiang, da Sala, da Bao'an, da Kazak da sauransu, wadanda musulmai ne.

A biyo mu cikin wannan shiri, don jin ta bakinsa kan yadda musulmai a wurin suka gudanar da azumi da ma shagulgulan bikin karamar sallah.