logo

HAUSA

Sin za ta kara rage haraji da sauran kudaden da kamfanoni ke biya

2021-05-11 10:53:23 CRI

Sin za ta kara rage haraji da sauran kudaden da kamfanoni ke biya_fororder_减税

Hukumar raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin, ta ce kasar za ta kara rage haraji da kudaden da ake biya domin bunkasa karfin harkokin kasuwanci.

Wata sanarwa da hukumar da wasu ma’aikatu 3 suka fitar, ta ce kasar Sin za ta samar da kudin da za su taimakawa harkokin kasuwanci da rage tsadar wasu kudade da gwamnati ta kakaba da na samar da kayayyaki ga kamfanoni.

Har ila yau, za a rage tsadar kayayyakin da kamfanoni ke bukata na gudanar da ayyukansu da sokewa ko rage wasu kudaden da ake biya a kan manyan hanyoyi da tashoshin jirage, domin inganta muhimman kayayyakin da sufuri.  

Bugu da kari, za a yi kokarin inganta jarin da kamfanoni ke juyawa da tabbatar da tallafawa kanana da matsakaitan kamfanoni a kan kari. (Fa’iza Mustpha)