logo

HAUSA

An tura dakarun wanzar da zaman lafiya 300 don kare garin Bakouma a CAR

2021-05-11 11:02:22 CRI

An tura dakarun wanzar da zaman lafiya 300 don kare garin Bakouma a CAR_fororder_210511-Afirka ta tsakiya

MDD ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya 300 domin su taimaka wajen ceto garin Bakouma dake jamhuriyar Afrika ta tsakiya, kakakin MDD ya bayyana hakan.

A safiyar ranar Lahadi ne aka tura dakarun wanzar da zaman lafiyar zuwa garin na Bakouma, daya daga cikin garuruwan da matsalolin tsaro suka haifar da samun jinkiri a zabukan watan Disamba da Maris, Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana hakan.

Dujarric ya ce, dakarun wanzar da zaman lafiyar za su baiwa fararen hula kariya kana za su taimaka wajen shirya zaben majalisun dokokin kasar da aka tsara gudanarwa nan gaba cikin wannnan wata.

Dakarun wanzar da zaman lafiyar MDD uku sun mutu a watan Disamba a wani tashin hankali da ya barke a shiyyar, lamarin da ya sa aka dage gudanar da zabukan. (Ahmad)