logo

HAUSA

Jami’an tsaron Najeriya sun kubutar mutane 30 daga hannun masu garkuwa

2021-05-11 10:55:53 CRI

A ranar Litinin jami’an tsaron Najeriya sun yi nasarar ceto mutane 30 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a lokacin da suke sallah a masallaci a jihar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

A yayin wani aikin sintiri na hadin gwiwa tsakanin sojoji, da ’yan sanda, da sauran hukumomin tsaro, an cimma nasarar kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su, a cewar Gambo Isa, kakakin hukumar ’yan sandan jihar Zamfara.

Isa ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kimanin mutane 40 ne aka yi garkuwa da su a lokacin da suke gudanar da ibada a lokacin sallar Tahajjud da sanyin safiyar ranar Litinin, inda gungun maharan suka fito daga yankin Zurumi, wani garin dake kan iyakar jihar Zamfara, maharan sun kewaye masu ibadar ne a wani sabon masallaci.

Bayan kammala lissafa adadin, har yanzu akwai mutane 10 da ba a gansu ba, sai dai a cewar kakakin ’yan sandan ba su da tabbaci ko mutanen suna hannun ’yan bindigar ko kuma sun tsere ne zuwa wasu wurare na daban don neman mafaka.

Ya kara da cewa, har yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike game da garkuwar. (Ahmad)