logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya tattauna da jami’an Turkmenistan

2021-05-11 10:05:23 CRI

Ministan harkokin wajen Sin ya tattauna da jami’an Turkmenistan_fororder_210511-Wang Yi

Kasashen Sin da Turkmenistan a ranar Litinin sun cimma matsaya game da gina wani cikakken tsarin hadin gwiwa na shekaru biyar a tsakanin kasashen biyu.

An cimma yarjejeniyar ne a lokacin tattaunawar da ta gudana tsakanin mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da mataimakin firaministan gwamnatin kasar Turkmenistan, kana ministan harkokin wajen kasar Rashid Meredov, da kuma mataimakin firaminista Berdymukhamedov, a garin Xi'an, babban birnin lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Dukkan bangarorin biyu sun amince za su kara kyautatawa da kuma zurfafa hadin gwiwarsu a fannin samar da iskar gas, da kokarin lalibo wasu hanyoyin hadin gwiwa a sauran fannonin da ba su shafi albarkatu ba.

Bangarorin biyu sun cimma matsayar kafa wani cikakken tsarin hadin gwiwa na shekaru biyar tsakanin kasashen biyu da kuma karfafa hadin gwiwarsu game da batutuwan dake shafar samar da bayanai don tabbatar da tsaron kasa da kasa da kiyaye muhallin halittu. (Ahmad)