logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da baje kolin kasa da kasa na Hanyar Siliki karo na 5

2021-05-11 14:02:33 CRI

Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da baje kolin kasa da kasa na Hanyar Siliki karo na 5_fororder_王毅

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci bikin kaddamar da bikin baje kolin kayayyaki na kasa da kasa na Hanyar Siliki, karo na 5. Wato bikin baje koli da zuba jari da hadin gwiwa tsakanin yankuann gabashi da yammacin kasar Sin, da aka yi a birnin Xi’an na lardin Shaanxi a yau Talata.

Wang Yi wanda ya halarci taron ta kafar bidiyo, ya ce dukkan kasashe na fuskantar jan aikin bijirewa tasirin annobar COVID-19 da daidaita tattalin arziki da kare tsarin rayuwar al’umma. Don haka, akwai bukatar hada hannu don zurfafa hadin gwiwa karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da inganta farfadowa da ci gaban tattalin arzikin duniya, tun da wuri.

Ya kuma gabatar da wasu shawarwari 4 da suka hada da: tunkarar kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar da zurfafa hadin gwiwa a fannin kiwon lafiyar al’umma. Na biyu, mayar da hankali wajen dunkulewar kasashe da karfafa tubalin ci gaba na bai daya. Na uku, kiyaye moriyar juna da samar da ingantaccen dandalin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya. Shawara ta hudu ita ce, mayar da hankali kan raya muhalli da samar da ayyukan misali a fannin ci gaba mai dorewa.

Bakin da suka halarci bikin, sun yabawa hadin gwiwar Ziri Daya da Hanya Daya, wanda ya samu gagarumin sakamako. Kuma suna fatan zurfafa hadin gwiwa da Sin a muhimman bangarori da karfarar hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar COVID-19 karkashin shawarar da kuma inganta farfadowar tattalin arzikin yankuna da na duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)