logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Gaskiya ba ta buya

2021-05-10 21:50:53 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying, ta fada a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Litinin cewa, a cikin 'yan kwanakin nan, ana samun karin maganganun adalci da gaskiya, game da batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang a duniya, wanda ke nuna cewa gaskiya ba ta buya.

Kwanan baya, asusun nazarin harkokin zaman lafiya da makoma ta kasar Sweden, ta wallafa wani rahoto na musamman mai taken" Matakin tabbatar da kasancewar "Kisan gilla" a jihar Xinjiang na da boyayyiyar manufa", inda aka tona makircin Amurka da yammacin duniya, na yada jita-jitar faruwar "kisan gilla" a jihar Xinjiang.

Ban da wannan kuma, shafin yanar gizo mai zaman kansa na Amurka Counterpunch, ya wallafa wani sharhi mai taken "Waiwaye a kan Babban Laifi na " Kisan gilla",  inda aka nuna cewa, zargin da kasar Amurka ta yi, na wai ana aiwatar da “kisan gilla” a Xinjiang ba shi da wata hujja. (Mai fassara: Bilkisu)