logo

HAUSA

Yan sanda a Najeriya sun damke mutane 8 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne

2021-05-10 10:32:16 CRI

Yan sanda a Najeriya sun damke mutane 8 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne_fororder_210510-yan sandan Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, ’yan sanda sun yi nasarar kame mutane 8 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani sabon samame da suka kaddamar kan masu aikata muggan laifuffuka a jihar Osun dake yankin kudu maso yammacin kasar.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Yemisi Opalola, ta bayyana cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta jiya Lahadi cewa, ’yan sandan sun yi nasarar kama wadanda ake zargin ne a ranar Jumma’a, a kauyen Omo Ijesa dake jihar, bayan samun rahotanni na sirri.

Jami’ar ta bayyana cewa, gabanin wannan kame, binciken ’yan sanda ya nuna cewa, wadanda ake zargin, sun koma jihar Osun ne, bayan sun yi garkuwa da wata mace, don kaucewa shiga hannun ’yan sanda a jihar Benue.

Haka kuma, wadanda ake zargin sun buya a jihar Osun ne, domin su sasanta tare da neman kudin fansa, koda bayan sun kashe matar da suka yi garkuwa da ita.

Opalola ta bayyana cewa, za a mika wadanda ake zargin wadanda ke tsakanin shekaru 18 da kuma 25 da haihuwa ga hannun rundunar ’yan sanda dake jihar Benue, da zarar an kammala binciken farko kan laifin da ake zarginsu da aikatawa.  (Ibrahim Yaya)