logo

HAUSA

Li Keqiang ya jaddada muhimmancin maida hankali ga ingancin hajojin Sin da ikon su na takara a kasuwannin duniya

2021-05-10 21:31:01 CRI

Li Keqiang ya jaddada muhimmancin maida hankali ga ingancin hajojin Sin da ikon su na takara a kasuwannin duniya_fororder_微信图片_20210510211429

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a zage damtse wajen daga matsayin ingancin hajojin da ake sarrafawa a kasar Sin, tare da tabbatar da ikon hajojin, da ma hidimomin da kasar ke samarwa na takara a kasuwannin gida da na waje.

Li Keqiang, ya yi fatan aiwatar da wadannan matakai, za su baiwa tambura kirar kasar Sin matsayin karbuwa ga masu sayayya na gida, da ma na kasuwannin kasashen waje.

Firaministan na Sin wanda ya yi wannan tsokaci, albarkacin ranar tambarin kira wadda aka kaddamar yau Litinin a birnin Shanghai, ya kuma yi kira ga kananan hukumomi, da sassan gwamnatoci, da su maida batun ingancin hajoji gaban komai, su kuma karfafa matakan yayata tambarin kasa tsakanin al’umma, tare da baiwa kamfanoni jagoranci, ta yadda za su zamo masu gudanar da ayyukan su bisa kwarewa da sanin makamar aiki, ta yadda hakan zai karfafa gwiwar su, da ikon su na yin takara bisa daidaito a budaddiyar kasuwa.    (Saminu)