logo

HAUSA

Ministan kudi: Ghana za ta samarwa matasan kasar karin guraben aikin yi

2021-05-10 11:19:30 CRI

Ministan kudi: Ghana za ta samarwa matasan kasar karin guraben aikin yi_fororder_210510-Ghanaian youth

Gwamnatin kasar Ghana ta ce, za ta gaggauta aiwatar da shirinta na samar da ayyuka da sana’o’in dogaro da kai da nufin samar da damammakin guraben aikin yi ga matasan kasar, ministan kudin kasar Ken Ofori-Atta ya bayyana hakan.

Ministan ya fadawa taron manema labarai cewa, shirin na dala miliyan 200 dake tafe zai bunkasa fannoni masu zaman kansu da kuma kanana da matsakaitan kamfanonin kasar ta yadda za su samu damar kirkiro guraben ayyukan yi ga matasa.

Ya kara da cewa, baya ga wannan shirin, gwamnatin kasar za ta kaddamar da sabbin shirye shirye guda takwas nan da wasu watanni masu zuwa a fannonin kiwon lafiya, yawon bude ido, kasuwanci, aikin noma, da fannin samar da kayayyakin more rayuwa da nufin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar, wanda kuma hakan zai kara bada gudunmawa wajen samar da guraben ayyukan yi a kasar.

Alkaluma na baya bayan nan sun nuna cewa, rashin ayyukan yi a tsakanin matasan kasar ta yammacin Afrika ya karu da kashi 9.46 bisa 100 a shekarar 2020, idan an kwatanta da kashi 9.1 bisa 100 a shekarar 2019. (Ahmad)