Masar za ta samar da riga-kafin COVID-19 na kamfanin Sinovac a watan Yuni
2021-05-10 10:41:32 CRI
Ministar lafiyar kasar Masar Hala Zayed, ta sanar cewa, Masar za ta fara aikin samar da riga-kafin COVID-19 na kamfanin Sinovac a cikin gidan kasar a watan Yuni.
Da take jawabi a taron manema labarai a birnin Alkahira, ministar ta ce za a samar da kashin karfo na riga-kafin miliyan 2 a watan Yuni a kamfanin sarrafa kwayoyin halittu da aikin riga-kafi na kasar Masar wato (VACSERA).
Zayed ta fadawa ’yan jaridu cewa, kamfanin zai samu dukkan kayayyakin hada riga-kafin da ake bukata ya zuwa ranar 18 ga watan nan na Mayu, ta kara da cewa, za a samar da riga-kafin miliyan 40 a shekarar farko.
Zayed ta ce, an kulla yarjejeniyoyi guda biyu tsakanin kamfanin Sinovac da VACSERA a watan Afrilu, yarjejeniyar farko ta baiwa bangaren kasar Masar damar samun kwararru masana da za su taimakawa aikin samar da riga-kafin, sannan yarjejeniya ta biyu ta baiwa kamfanin VACSERA damar samun lasisin samar da riga-kafin.
Ministar ta ce, riga-kafin da kamfanin na Sinovac zai samar a kasar Masar za a dinga kiransa da sunan Sinovac-Vacsera. (Ahmad Fagam)