logo

HAUSA

Shugaba Xi ya yi kira da a bunkasa al’adun gargaji na al’ummar Sinawa

2021-05-10 21:06:22 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga al’ummar kasarsa, da su zage damtse wajen ba da gudumma a fannin ilimin falsafa, da kimiyyar zamantakewar bil adama, ta yadda hakan zai ingiza bunkasar al’adun gargaji na al’ummar Sinawa karkashin sabbin hanyoyi masu cike da basira.

Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wata wasikar martani da ya rubuta, zuwa ga editocin mujallar Chinese Humanities ta kasar.  (Saminu)